Rahotanni sun bayyana cewa an kama Akanta-Janar na Najeriya, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da karkatar da dukiyar gwamnati.
Premium Times ta ruwaito cewa jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC ne suka kama Akanta-Janar din a Jihar Kano kuma suka tafi Abuja da shi a Yammacin ranar Litinin.
- Hukumar ’Yan sandan Najeriya ta yi wa Magu karin girma
- ‘Yan bindiga sun kashe Sojoji biyu, sun kone Kotu a Anambra
Majiyar rahoton ta ce Hukumar EFCC ta dade tana gudanar da bincike kan wani al’amari na karkatar da kudaden gwamnati da suka kai kimanin Naira biliyan 80 da ake zargin an karkatar da su ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.
Kamfanonin da aka yi amfani da su wajen karkatar da kudaden, ana zargin cewa suna alaka da wasu ‘yan uwa da abokan Babban Akantan, a cewar masu binciken.
Majiyar ta bayyana cewa Hukumar EFCC ta shafe tsawon lokaci tana aike wa da Babban Akantan goron gayyata amma yana yin buris da ita.
“Mun dade muna gayyatar shi amma ya ci gaba da nokewa,” a cewar majiyar.
“Ba mu da wani zabi da ya wuce mu kama shi mu tsare shi.”
Wani babban jami’in EFCC da ya bukaci a sakaya sunansa saboda rashin samun izinin tattaunawa da manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya zuwa hada wannan rahoto ba a iya jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ta EFCC ba, sai dai wani na kusa Akanta-Janar din ya ce an an kama shi yana shirin tafiya Ingila.
Ana iya tuna cewa a raar 25 ga watan Yunin 2015 ne Shugaba Muhammad Buhari ya nada Mista Idris a matsayin Akanta-Janar na Najeriya.
Kafin wannan lokaci babu mai rike da mukamin tun bayan da tsohon Akanta-Janar, Jonah Otunla, ya sauka daga kujerar a ranar 12 ga watan Yuni, 2015.
Shugaba Buhari ya sake nada Mista Idris wa’adi na biyu na tsawon shekaru hudu a watan Yunin 2019, a daidai lokacin da Kungiyoyin Kwadago suka nemi Akanta-Janar din ya yi murabus bayan ya cika shekara 60 da haihuwa.
An haifi Mista Idris wanda dan asalin Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya a ranar 25 ga watan Nuwamban 1960.
Gabanin nadinsa a matsayin Akanta-Janar a shekarar 2015, shi ne Daraktan Kudi da Asusu a Ma’aikatar Ma’adinai da Karafa ta Tarayya.