✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Lantarki Olu Agunloye

An gurfanar da tsohon ministan kan zargin zamba da almundahana.

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Mista Olu Agunloye a gaban kotu.

EFCC ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya, bisa zarge-zargen zamba da almundahana.

Mista Agunloye wanda aka gurfanar a gaban kotu a wannan Larabar, bai amsa laifin da ake tuhumarsa da su ba.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje, har zuwa lokacin da za a bayar da belinsa.

Ana iya tuna cewa, a watan Disambar 2023 ne EFCC ta bayyana Agunloye a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin almundahana.

A cikin sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X (Twitter), ta sanya hoton tsohon ministan tare da yin kira ga jama’a da su ba da bayanan da za su kai ga kama shi.

Gurfanar da shi na zuwa ne bayan gayyatar tsofaffin ministocin ma’aikatar jin-kai, Sadiya Umar Farouq da Betta Edu kan zargin almundahanar sama da biliyan 40.

Tuni dai EFCC ta gayyace su domin amsa tambayoyin kan zargin da ake musu.

Daga bisani kuma hukumar ta karbe fasfo din su, domin hana su fita dafa Najeriya har zuwa lokacin da za a kammala binciken.