Hukumar Yaki da Ma su Yi wa Tattalin Arziki Kasa Zagon-kasa a Najeriya (EFCC) ta gurfanar da tsohon Akanta Janar na Jihar Legas, Olasupo Shasore bisa zarginsa da almundahana.
A ranar Juma’a ne dai aka gurfanar da tsohon Kwamishinan Shari’ar a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tare da kamfaninsa mai suna Middlesex Investments.
- ’Yan uwan Gwamnan Sakkwato sun sauya sheka daga jam’iyyarsa
- Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram sun cafke 27
Gwamnatin Tarayya ce ke karar, inda lauyan EFCC Bala Sanga ke wakiltar ta a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/386/22.
Sai dai ya musanta zargin, inda Mai shari’a Ekwo ya dage shari’ar zuwa rana 13, da 14, da 15, da 16, da 17 ga watan Maris na badi.
EFCC ta ce Shasore da kamfaninsa sun gaza ba ta bayanai a rubuce kan shigar Naira miliyan 60 asusun kamfanin daga kamfanin Mandivera Global Resources zuwa asusun Middlesex a tsakanin ranar 3 ga Satumba zuwa 11 ga Satumban shekarar 2014.
Har ila yau, EFCC ta yi zargin cewa tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 3 ga watan Satumbar 2019, wadanda ake tuhumar sun gaza bai wa hukumar bayani a rubuce kan zunzurutun kudi Dala 30, 000 daga asusun kamfanin na Middlesex Investments da aka tura zuwa asusun Olasupo Shasore.
Hukumar ta ce hakan ya saba wa sashe na 10(1)b na dokar hana safarar kudade ta 2011, wanda ya tanadi hukunci karkashin sashe na 10(3) na wannan dokar.
Haka kuma ana ci gaba da tuhumar wadanda ake zargin da kin bin ka’idojin mika wa Ma’aikatar Kula da Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya, rahoton ayyukan kamfanin, wanda ya saba wa Kundin Dokar haramta almundahana na 2011.