✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gaza gabatar da hujja a kan Kwankwaso a kotu

Lauyan EFCC ya buƙaci kotun ta ba su lokaci domin shiryawa.

Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziƙi Ta’annati (EFCC) ta kasa gabatar da takardu a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, wanda hakan ya kawo jinkiri a sauraron shari’ar tsakanin hukumar a da jagoran Jami’yyar NNPP na Kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai.

Masu shigar da ƙarar sun haɗa da NNPP, Dokta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Injiniya Buba Galadima da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

EFCC ce wadda ake ƙara a wannan shari’ar.

Lauya masu ƙara, Robert Hon, ya ce a shirye suke domin ci gaba da shari’ar.

Ya nuna cewa EFCC na da kwana biyar don shirya wa shari’ar, amma fiye da kwana 30 ta wuce ba tare da sun shirya ba.

Hon, ya bayyana cewa wannan shari’ar ta shafi ‘yancin ɗan adam ne, inda kuma ya roƙi kotu ta yi watsi da buƙatar EFCC na jinkirta shari’ar ba saboda ba su bayar da ƙwaƙƙwaran dalili.

Lauyan EFCC, Idris Ibrahim Haruna, ya nemi kotun ta ƙara musu lokaci domin su shirya amsarsu.

Alƙalin kotun, Mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, 2024, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

A baya kotun ta haramta wa EFCC kama ko tsoratar da waɗanda suka shigar da ƙara har sai an kammala shari’ar.