Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), ta ce ta gano ma’aikatan bogi a hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya har dubu 37 da 395, inda hakan ya jawo wa gwamnati asarar kimanin Naira biliyan daya.
Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da yake jawabi a wajen bude wani taron fadakarwa da aka shirya wa ma’aikatan sashin ayyuka da gidaje a Abuja.
Malam Ibrahim Magi ya ce baya almundahanar da ake tafkawa a ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati, matsalar ma’aikatan bogi na matukar damun hukumar.
Ya ce: “Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi dubu 37 da 395 a cikin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, kuma ana ci gaba da bincike. Sannan bincikenmu yanzu haka ya gano cewa Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kimanin Naira biliyan daya ga wadannan jabun ma’aikata. Tabbas adadin yana iya karuwa a yayin da za mu dada bankado ma’aikatan bogi da aka binne a cikin tsarin biyan albashi na Gwamnatin Tarayya.”
Magu ya ce hukumar ta kafa sashin yaki da almundhana kan bayar da kwangila domin kula da koke-koken da ake yawan samu kan keta dokokin bayar da kwangila. Sai ya shawarci ma’aikatan gwamnati su guji yin duk wani abu da ya saba wa dokokin bayar da kwangila, ya ce masu karya dokokin za su fuskanci zaman kurkuku da korar kare daga aiki.
A jawabin Babban Sakataren (Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje), Abubakar Magaji, ya ce a matsayinsu na direbobin jagorantar tsare-tsaren gwamnati, wajibi ne hukumomi da ma’aikatun gwamnati su zamo a sahun gaba wajen bin dokoki da ka’idojin aiki. Ya ce sashin ayyuka da gidaje ya yanke shawarar zai rika shirya fadakarwa ga ma’aikata kan muhimmancin bin dokoki da ka’idoji.
EFCC ta gano ma’aikatan bogi dubu 37 a ma’aikatun tarayya – Magu
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), ta ce ta gano ma’aikatan bogi a hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya har dubu 37…