Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta gano kusan Dala biliyan daya da rabi (kimanin Naira biliyan 548) da take da yakinin na haram ne a wani asusun banki na kasar Switzerland da ake zargin na tsohuwar Ministar Man fetur ce Misis Diezani Allison-Maduake a ci gaba da binciken da hukumar ke yi a kanta.
Wannan bayani yana zuwa ne bayan wasu bayanai sun ce Najeriya tana kokarin inganta wasu yarjejeniyoyi da Daular Laraba don kwato wasu gidajen kasaita da ake alakanta su da tsohuwar Ministar. Wata majiyar EFCC ta ce, wadansu masu bincike sun kai ga wasu gidajen kasaita biyu da ake zargin na tsohuwar Ministar ce a birnin Dubai da ke Daular Larabawar kafin fara aiki da shirin Gwamnatin Tarayya na mallaka wa gwamnati kadarorin. Gidajen dai suna lamba na E146 Emirates Hill, Dubai da lamab J5 Emirates Hill Dubai.
Masu bincike su hudu sun bar Najeriya a ranar Juma’ar da ta gabata domin nemo karin bayani kan dukiyar da ake zargin Alison-Madueke da wawura.
Majiyar Hukumar EFCC, ta yi zargin cewa kudaden haram din suna da alaka da tsohuwar Ministar da abokan harkarta hudu. Kuma abokan harkarta sun yi amfani ne da wasu kamfanonin Shell biyu don sayar da danyen maid a ya kai Dala biliyan 1.5, kuma a cewar majiyar an gano kudin ne a wani asusun ajiyar banki a kasar ta Switzerland.
Majiyar ta ce,zuwa yanzu bincike ya gano cewa an wawure Dala biliyan 1.5 da aka boye a asusun na Switzerland bayan an batar da sawunsu ta bi ta Amurka. Kuma hukumar tana da bayanan yadda kamfanonin mai suka shigar da kudaden cikin asusun.
Hukumar ta ce bincike ya tabbatar da cewa an yi amfani da asusun ne wajen sace kudin domin a sayi kadarori masu tsada a Najeriya da sauran sassan duniya. Kuma bangaren shari’a na Amurka ta hannyn shirin kwato dukiyar sata na Kleptocracy yana kokarin kwato Dala miliyan 144 na kadarori daga wadansu abokan harkar Diezani.
Bayanai sun ce gidajen kasaitar biyu na Misis Alison-Madueke da aka gano a Dubai sun kai Dirhami miliyan 74, (kimanin Naira biliyan7 da miliyan 212 da dubu 831 da 800).
A watan ranar 19 ga Janairun shekarar 2016 ne Shugaba Buhari ya kulla yarjejeniyoyi shida da Daular Larabawa kan yadda za a taimaka wajen kwato dukiyar sata da ’yan Najeriya suka kai kasar.