Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC), ta tabbatarwa da kotu cewa ta damke Faisal, dan tsohon shugaban kwamatin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina.
EFCC ta ce a daren Alhamis jami’anta suka cafke Fasail mai shekara 21, wanda kotu ta bayar da belinshi ranar 24 ga wantan Yuni bayan tsare shi da jami’an tsaro suka yi.
- Ganduje ya yi ta’aziyyar mutanen Dambatta 16 da aka harbe
- Ku bar Adamawa ko ku fuskanci hukuncin kisa —Fintiri ga ’yan bindiga
- COVID-19 ta kashe Janar din Sojin Najeriya
Faisal na fuskantar shari’a ne a gaban Babbar Kotu a Abuja, wadda ta shelanta nemansa ruwa a jallo saboda ya yi batar dabo da ta ba da belin shi.
Matashin na fuskantar laifuka uku dake da alaka da badakalar kudade.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Abang, a ranar 24 ga watan Nuwamba ya soke belin da da ya bayar na Faisal, dukda cewa daman akwai batun umarnin da aka ba jami’an tsaro kan su kamo shi duk inda yake.