Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, sa’o’i kadan bayan ya mika mulki ga magajinsa.
Wani jami’in EFCC ya shaida wa wakilinmu cewa sun tsare Mista Obiano ne da misalin karfe 8.30 na dare a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, a yayin da tsohon gwamnan yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Amurka ranar Alhamis.
- Duk wanda ya sa N5m a banki a sanar da EFCC —Majalisa
- Matar tsohon Gwamnan Anambra ta tsinka wa matar Ojukwu mari a wajen rantsuwa
Ya bayyana cewa tun kafin saukar Obiano daga mulki yake cikin jerin mutanen da EFCC ke nema su amsa tambayoyi kan zargin wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar gwamnati, amma rigar kariyar kujerar gwamna ta hana hukumar yin hakan.
Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar wa wakilinmu cewa hukumar na tsare da tsohon gwamnan, amma bai yi karin bayani ba.
Matar Obiano ta gaura wa matar Ojukwu mari a wurin taro
A ranar Alhamis din da aka tsare Obiano ne dai ya mika ragamar shugabancin Jihar Anambra ga sabon gwamnan jihar, Farfesa Charles Soludo.
Aminiya ta kawo rahoton wata dambarwa a wurin taron rantsar da sabon gwamnan, inda Misis Ebelechukwu, matar Obiano, ta gaura wa matar tsohon madugun ’yan tawayen Biyafara, Bianca Ojukwu, mari ana tsaka da bikin.
Matar ta Obiano ta gaura wa Bianca Ojukwu marin ne jim kadan bayan an kammala rantsar da Farfesa Soludo domin kama aiki gadan-gadan.
Manyan baki na zazzaune lokacin da Misis Ebelechukwu Obiano ta tashi takanas zuwa inda Bianca take zaune, sannan ta tsinka mata mari.
Lamarin dai ya jawo hayaniya, daga bisani jami’an tsaro suka yakice Ebelechukwa daga jikin matar Ojukwun, suka fita da ita daga wajen taron, daga baya mijin nata ya fice, tun da an riga an kammala rantsar da sabon gwamnan.