✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta cafke garin kudi na N11m a hannun masu sayen kuri’u

An kama wadanda ake zargin ne a wannan Asabar din yayin wani samame da aka yi ta hanyar leken asiri.

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da sayen kuri’u a rumfunan zabe a kananan hukumomin Otueke da Adawari da ke Bayelsa da kuma rumfunan zabe daban-daban a Imo da Kogi.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a wannan Asabar din yayin wani samame da aka yi ta hanyar leken asiri da aka fara kwanaki kadan gabanin zaben gwamnoni da ake gudanarwa a jihohin uku.

“Jami’anmu sun kwato jimillar tsabar kudi har N11,040,000, wanda suka kunshi N9,310,00 da aka kama daga hannun wadanda ake zargi da saye da sayar da kuri’u a Bayelsa.

“Akwai kuma N1,730,000 da aka kama daga hannun wadanda ake zargi da magudin zabe a Jihar Imo.

“Haka kuma an kama motoci biyu daga hannun wadanda ake zargin. Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.