Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta mai ɗauke da hoton tsohon gwamnan.
Matakin hukumar na zuwa ne ’yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.
Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC, Kemi Phinro ya faɗa mata cewa “wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka.
“EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2.”
Sanarwar ta kuma buƙaci duk wani mai bayani game da inda tsohon gwamnan yake ya gaggauta kai mata rahoto ko ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Tun a jiya Laraba rahotanni suka ce gwamnan Kogi na yanzu, Usman Adodo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami’an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.
Kawo yanzu dai Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin.
Lauyan hukumar ya kuma ce suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar sojin Najeriya wajen kamawa tare da gurfanar da shi a gaban kotun.