✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC na tuhumar mai kamfanin wallafa littattafai na Macmillan kan damfarar N65m

Sai dai wanda ake zargin ya cika wandonsa da iska

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na tuhumar mai kamfanin wallafa littattafai na Macmillan, Farfesa Adesanye Adelekan, kan badakalar  damfarar Dalar Amurka 156,700, wato kwatankwacin Naira miliyan 65.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana tuhumarsa ne tare da wani mai suna Bola Fasasi.

EFCC dai ta sami nasarar kamo Fasasi a Jihar Legas ranar Litinin, sai dai Adesanye, ya ranta a na kare.

An dai gurfanar da mutanen biyun a gaban wata kotun manyan laifuka da ke Ikeja, da tuhume-tuhume shida da suka hada da karbar kudi ta hanyar yaudara.

Hukumar a kunshin karar ta ce: “Mamallakin kamfanin wallafa littattafai na Macmilian, Farfesa Adesanya Iyiola Adelekan, da yanzu ya cika wandonsa da iska, ya hada kai da Fasasi Bola, inda suka karbi littattafan sayarwa da darajarsu ta kai Dala 156,711.87, ta hanyar yaudara daga kamfanin BHS Book Printing SDN BHD na Selangor da ke Malesiya, da alkawarin siyar da littattafansu tura kudin da aka samu a cinikin sati biyu bayan shigar rasiti hannunsu.”

To sai dai Fasasi ya musanta wannan zargin, kuma alkalin ya ba da umarnin tsare shi a gidan kason da ke Ikoyi, hadi da dage zaman shari’ar zuwa ranar 7/7/2022 domin jin yiwuwar ba da belinsa.

Idan za a iya tunawa dai Hukumar ta EFCC a shekara ta 2018, ta taba tsare Adelekan bisa zargin hannunsa a badakalar hukumar kula da ilimin matakin farko, a samar da kayyakin binciken kimiyya da fasaha da kuma littatafan karatun ‘yan makaranatun hadaka 104 a kasar nan.