✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC na binciken manyan ma’aikatan zabe a Sakkwato

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) a yau Talata ta ziyarci cibiyar ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa…

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) a yau Talata ta ziyarci cibiyar ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) daga nan jami’an EFCC suka wuce da wasu manyan ma’aikatan hukumar zaben don amsa wasu tambayoyi.

Wasu daga cikin manyan jami’an EFCC sun tabbatar da binciken da ake yi wa ma’aikatan zaben, amma ba a bayyana cikakken dalilin yin binciken ba.

A kwanakin baya ne aka fitar da wani rahoton da yake cewa jami’an EFCC sun kama ma’aikatan zabe hudu wadanda ake tuhumar su da karkatar da kudaden ma’aikatan wucin gadi na zaben 2019 da aka yi wanda ya kai Naira miliyan 84.6.