Kungiyar Matasan Arewa (AYA), ta ce a shirye take ta yaki duk wai mai yin barazana ga Shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annaci (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Kakakin kungiyar ta AYA, Mohammed Salihu Danlami ne ya bayyana haka, a lokacin wani gargadi da ya yi a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna, ranar Laraba.
- ’Yan bindiga sun sace dalibai, sun harbi wasu a Kebbi
- Saudiyya ta kashe matashi kan laifin da ya aikata yana karami
“A shirye muke mu yaki duk wani mutum ko gungun mutane da ke yi masa barazana.
“Duk wani hari ko wata barazana da za a yi wa Shugaban na EFCC, to barazana ce a gare mu kuma za mu binciko yin mai barazanar mu kuma yi amfani da doka wajen gurfanar da shi.
“Bai kamata a dauki wannan barazanar da wasa ba. Mu matasan kasar nan muna goyon baya da girmama shugaban tun daga lokacin da aka nada shi kuma a shirye muke mu goyi bayansa don cimma nasarar aikinsa.
Kungiyar ta jaddada cewa barazanar da ake wa Shugaban na EFCC wani koma baya ne ga yaki da rashawa.
Danlami ya kara da cewa, “Kudin da za a yi amfani da su don samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, hanyoyi, da sauransu duk wasu tsirarun mutane sun wawushe. Burinmu shi ne ganin yadda za a kawo karshen rashawa a Najeriya.”