Rahotanni sun ce an dakatar da mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) Ibrahim Magu daga mukaminsa.
An ruwaito majiyoyi daga fadar shugaban kasa na cewa Fadar Shugaban Kasar ce ta dakatar da shi a ranar Talata, washegarin ranar da ya fara bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin binciken zargin almundahana a EFCC karkashin shugabancinsa.
Sai dai zuwa yanzu dai babu tabbaci daga fadar shugaban kasa ko wasu hukumomin gwamnati game da dakatarwar. Wakilinmu ya tuntubi EFCC domin samun karin bayani, amma babu wani haske.
A ranar Litinin Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin karkashin Tsohon Mai Shari’a Ayo Salami domin gabatar da bayanansa game da binciken kwamitin kan kadarorin gwamnatin da aka kwato. Wasu majiyoyi na cewa ya kwana a tsare saboda ba a kammala binciken ba.
A ranar Litinin ne rahotanni suka yi ta cewa hukumar DSS ta tsare shi, kafin daga bisani DSS da fadar shugaban kasa da ma EFCC su karyata.
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce ba tsare Magu aka yi ba amma, “Shugaban EFCC ya bayyana a gaban kwamitin shugaban kasa kan kadarorin da aka kwato ne domin amsa wasu tambayoyi”.