Da alama rikicin da ake fama da shi tsakanin Gwamnan Edo, Godwin Obaseki da Mataimakinsa, Philip Shaibu, ya dauki sabon salo bayan an mayar da ofishin mataimakin wajen gidan gwamnatin Jihar.
Bayanai sun nuna ofishin, wanda a baya yake cikin gidan gwamnatin a Benin City babban birnin Jihar, a yanzu an mayar da shi wani gini da ke kan titin Dennis Osadebey a cikin birnin.
- ‘Dalilin da Tinubu ya yi wa dukkanin Jakadun Najeriya kiranye’
- Ba za mu janye dokar hana dalibai mata sanya abaya a makarantu ba — Faransa
Tuni dai aka kafa allon da ke dauke da rubutun “Ofishin Mataimakin Gwamna” a mashigar ginin.
Da aka tuntube shi, Kwamishinan Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a na Jihar, Chris Nehikare, ya ce, “Idan dai ta tabbata akwai allon a kafe a wajen, to haka ne ke nan.”
Rikici tsakanin mutanen biyu dai ya fara ne a kan yunkurin Philip na neman kujerar lamba daya a jihar, matakin bisa ga dukkan alamu Obaseki bai yi na’am da shi ba.
Philip dai ya fito ne daga yankin Arewacin Edo, na neman ya gaji Obaseki ne, wanda ya fito daga Kudancin Edo, amma shi kuma ya fi son wani daga Edo ta Tsakiya.