✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Edo 2020: Babu shirin dage Gasar Wasanni Ta Kasa saboda cutar Kurona – Minista Dare

Minitsan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa za a dage Gasar Wasanni ta Kasa, ta bana (Edo 2020)…

Minitsan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa za a dage Gasar Wasanni ta Kasa, ta bana (Edo 2020) saboda tsoron yaduwar cutar Kurona; inda ya ce za a ci gaba da shirin gudanar da gasar kamar yadda aka shirya.

Ministan ya bayyana haka ne ta bakin Daraktan Shirye-Shirye kuma Mamba na Kwamitin Shirya Gasar, Mista Peter Nelson inda ya ce “Gasar Edo 2020 tana ba fashi, kamar yadda aka shirya.

“Babu wanin abin damuwa, domin tuni Minista ya sanya an ware wani wuri na musamman don killace duk wanda aka samu ya kamu da cutar Kurona.

“Daraktan Lafiya yana aiki tare da hukumomin Jihar Edo don tabbatar da an yi kyakkyawan tanadi a kan wannan cuta. Don haka ba mu da wata shakka kan samun nasara a cikin shirinmu.”

“Jita-jitar da ake yadawa kan dage wannan wasa abar takaici ce. Kuma muna ganin wadansu magabta ne suke baza ta don kawo cikas ga shirinmu na yin gasar cikin nasara,” inji shi.

Ya ce Minitan ya je ya duba ingancin wurare da kuma kayan wasanni tun makon jiya, kuma shirye-shirye sun kammala don tabbatar da gudanar gasar ta Edo 2020.

Domin tabbatar da samun nasarar gasar, Ministan ya gana da Ma’aikatan Ma’aikatar Lafiya a makon jiya da kuma wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) don tabbatar da an sanya matakan kare yaduwar cututtukan da aka iya dauka ta cudanyar jama’a irin su cutar tarin fuka da sauransu.

Shugaban Kwamitin Aiwatar da Shirye-Shiryen Gudanar da Gasar na Jihar Edo, kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Mista Philip Shu’aibu ya ce “Jihar Edo a shirye take ta dauki nauyi bakuncin wannan gasa ta kasa mai tarihi. Kuma wannan yana nuna Edo ta sake karbar kambinta na dauri da aka santa da shi a fagen wasanni.”

Ana sa ran za a fara gasar daga ranar 22 ga watan Maris zuwa 1 ga Afrilun bana.