Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta cire takunkumin da ta kakaba wa kasar Mali sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agusta.
ECOWAS ta alakanta matakin da ta dauka kan irin ci gaban siyasar da ta ce Mali ta samu yayin da abubuwa ke kokarin komawa kamar a baya.
Kungiyar a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta ce cire takunkumin na zuwa ne kwanaki kadan da nada fitaccen jami’in huldar diflomasiyyan kasar, Moctar Ouane a matsayin sabon Fira Minista.
Ta kuma yi kira ga gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta saki dukkannin sojoji da fararen hular da suka kama bisa zarginsu da hannu a juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.
Kungiyar ta kuma yi kira da a rushe majalisar sojojin kasar da ta jagoranci juyin mulkin.
Gwamnatin rikon kwaryar Mali na karkashin Shugaba Bah N’Daw wanda tsohon ministan tsaro da kuma Assimi Goita a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Gwamnatin dai na da watanni 18 ta shirya zabe tare da mika ragamar shugabanci ga sabuwar zababbiyar gwamnati.