✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Atletico Madrid a Uyo

A ranar 21 ga watan Mayun wannan shekara ce ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da…

A ranar 21 ga watan Mayun wannan shekara ce ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da kulob din Atletico Madrid na Sifen.  Za a yi wasan ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke garin Uyo na Jihar Akwa Ibom.

Kocin Super Eagles Gernot Rohr ne ya sanar da haka a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake hira da kafar watsa labaran wasanni ta Supersport a shirye-shiryen da kungiyar ke yi na halartar gasar cin kofin duniya a Rasha.

Kocin ya ce za a gudanar da wasan sada zumuntar a garin Uyo ne don kungiyar Super Eagles ta nuna godiya ga irin karamci da gwamnati da al’ummar Jihar Akwa Ibom musamman na garin Uyo suka nuna wa kungiyar a lokacin da ta gudanar da wasannin neman hayewa gasar cin kofin duniya a filin wasa na Godswill Akpabio.

“Mun shirya wasan sada zumunta da Atletico Madrid ne a garin Uyo don nuna godiya da karamcin da mutanen Uyo suka nuna wa Super Eagles a yayin da muka gudanar da wasanninmu a can”, inji Rohr.

Sai dai kocin ya nuna zai yi amfani da mafi yawa daga cikin masu yin kwallo a gida (home based) ne a yayin wasan, amma duk da haka zai gayyaci wasu daga cikin ’yan kwallonsa da ke wasa a kasashe daban-daban na duniya.  Ya ce zai yi haka ne a kokarin tantance aihinin ’yan kwallon da zai tafi da su gasar cin kofin duniya a Rasha.

Haka kuma ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasannin sada zumunta da kasashen Dimokuradiyyar Kongo da Ingila da kuma Czech Republic kafin a fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yunin wannan shekara a Rasha.

Super Eagles za ta fafata ne da kasashen Ajantina da Iceland da kuma Kuroshiya a zagayen farko a gasar cin kofin duniya a Rasha.