Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kirkiro da kudin intanet na e-Naira bayan ta haramta hada-hadar Cryptocurrency.
Kudin dai za su ba mutane damar hada-hadar cinikayya a tsakaninsu ta intanet.
- Kurunkus: Jirgin karshe dauke da dakarun Amurka ya bar Afghanistan
- JAMB ta soke mafi karancin makin shiga manyan makarantu na bana
CBN dai a baya ya ce ya dakatar da amfani da Cryptocurrency ne saboda ba wata kasa ce ta kirkiro shi a hukumance ba.
Za a dai kaddamar da fara amfani da kudin ne daga ranar daya ga watan Oktoban 2021.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani a kan sabon kudin:
- Sabon kudin zai bayar da damar cinikayya, amma ya bambanta da kowanne irin kudi na intanet saboda hukuma ce za ta kirkiro shi ta hannun CBN.
- Kudin zai bambanta da sauran kudaden intanet na Cryptocurrency irinsu Bitcoin.
- Zai taimaka wa burin bankin wajen taimaka wa tattalin arziki da kuma taimaka wa rage amfani kudade na takarda.
- e-Naira, kudin da aka kirkira don hada-hadar intanet, ba ya bukatar kudade na zahiri.
- Darajarsu ba za ta rika hauhawar ba gaira ba dalili ba kamar na Cryptocurrency, kuma zai yi aiki kamar yadda Naira ta takarda take aiki.
- Kudin, darajarsu za ta kasance iri daya da ta Naira, kuma za su rika tafiya kafada da kafada.
- Za a kirkiri asusun ajiyarsu a banki daban da asusun ajiyar sauran kudade, kuma cibiyoyin hada-hadar kasuwanci ne za su bude asusun ta hanyar wata manhaja.
- Za su kasance halastattun kudade na kasa baki daya, ba za su rika amfani da kudin ruwa ba kuma CBN ne zai rika kula da hada-hadarsu da kuma iyakar abin da za a iya kashewa a kullum.
- Kasancewarsu muhimman kadarorin kasa, za a samar wa da kudaden cikakken tsaro, a kuma adana dukkan bayanan sirri na masu amfani da su saboda kaucewa masu kutse.