Wani bincike da Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Duniya (WMO) ta gudanar ya gano cewa idan ba a yi da gaske ba, duniya na iya fuskantar matsanancin yanayin zafi sama da na yanzu, nan da shekara biyar masu zuwa.
Hukumar ta ce yanayin zafin zai iya karuwa da makin celcius 1.5 da ake kokarin kaucewa, wanda hakan ya sa aka shiga fargaba.
- 2023: Ba mu muka saya wa Jonathan fom din takara a APC ba — Miyetti-Allah
- TETFUND zai raba fiye da N1bn ga manyan Makarantu a Najeriya
Masana kimiyya sun ce ko da sau daya a shekara aka samu yanayin da ya zarta maki 1.5, akwai babban hadari tare da narkewar kankara kan teku da kuma ambaliya.
WMO ta ce karya dokokin da aka kafa a yarjejeniyar sauyin yanayi na birnin Paris ko da sau guda ne, na iya haifar da matsalar da za a jima ana shan azaba na dumamar yanayi.
An jima dai ana gudanar da taruka kan shawo kan matsalar da ke kara haifar da dumamar yanayi, wanda kasashe suka dauki matakai daban-daban don magancewa.