✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dukan malamai: Kotu ta yanke mata hukuncin share makaranta na wata 6

Sai dai kotun ta ba da zabin biyan tarar N30,000, wadanda za a ba malaman da aka ci zarafin nasu

Wata kotun Majistare da ke zamanta a garin Ota na Jihar Ogun, ta umarci wata mata da ta share harabar makarantar Iju-Ebiye na tsawon wata shida, saboda tura ’yan daba su daki shugaban makarantar.

Matar, mai suna Biola Joshua mai kimanin shekara 40 dai, ana zarginta ne da daukar hayar ’yan daba zuwa makarantar don cin zarafin malaman.

Tun da farko dai, ’yan sanda sun tuhume ta da laifin hada baki, cin zarafi da kuma tayar da zaune tsaye.

’Yar sanda mai shigar da kara, Insfekta Cynthia Ejezie, ta shaida wa kotun cewa wacce ake zargin tare da dan nata da wasu da yanzu haka suka cika wandonsu da iska sun aikata laifin ne da misalin karfe 2:00 na ranar 11 ga watan Maris din 2022 a makarantar ta Iju-Ebiye.

Insfekta Cynthia ta kuma ce wacce ake zargin da sauran wadanda suke tare dai sun lakada wa shugaban makarantar da kuma malamin da ke kula da lafiyar dalibai dukan kawo wuka.

Hakan, a cewarta ya sa sun samu munanan raunuka a jikinsu, baya ga tayar da hankulan dalibai suna tsaka da karatu a cikin makarantar.

Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Shotunde Shotayo, ta umarci matar da ta share makarantar kullum tun daga karfe 8:00 na safe har zuwa 11:00 na safe, tsawon wata shida.

Sai dai ta ba da zabin biyan tarar N30,000 a maimakon sharar, wadanda za a ba malaman da aka ci zarafin nasu.