Wata Kotun majistare a Jihar Kano, ta umarci ’yan sanda su binciki zargin dukan da dan Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa, ya yi wa wakilin jaridar Leadership a Kano
Kotun mai lamba 24 mai zamanta a unguwar Gyadi-gyadi ta umarci Mataimakin babban Sufeton ’Yan Sanda na shiyya ta daya da ke Kano, da ta binciki lamarin.
- An ba hammata iska tsakanin Doguwa da Garo a Kano
- Kano ta Kudu: Shin Alhassan Doguwa ya ci amanar Kabiru Rurum da Kawu Sumaila?
Umarnin na kunshe ne a cikin wata wasika da kotun ta aika wa shugaban shiyyar wacce magatardar kotun ya sa hannu a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Hakan ya biyo bayan koken da dan jarida Abdullahi Yakubu ya shigar ta hannun lauyoyinsa Bashir Umar & co a inda ya ke neman kotun da bi masa hakkinsa na cin zarafi da Doguwa ya yi masa ta hanyar dukan sa a yayin gudanar da aikinsa a gidan dan majalisar.
Dan jaridar wanda shi ne babban jami’in kula ofishin jaridar a Kano, ya yi zargin cewa dan majalisar ya naushe shi a yayin da shi da abokan aikinsa ke bakin aikin hira da dan majalisar a gidansa.
Haka kuwa ta faru me yayin da dan jaridar ya tambayi dan majalisar yadda aka yi ya daki Murtala Sulen Garo a yayin wani taro a gidan mataimakin gwamnan Kano.
Dan majalisa Alhassan Ado aka ce, ya fusata a yayin hirar, ya kuma naushi Abdullahi Yakubu wanda a cewarsa, ta kai ga yanzu ba ya ji sosai da kunnensa guda daya.
Lauyoyin sun bukaci da ta gudanar da binciken ne domin daukar mataki na shari’a kan dan majalisar.