Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jami’yyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar cewa duk yadda sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar ya kasance zai karbe shi hannu biyu.
Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya sanar da hakan ne yayin jaddada cewa yana matukar mutunta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma girmama shi.
- Ayyukan da Buhari ya aiwatar a Spain kafin dawowarsa Najeriya
- An kafa hukumar kula da amfani da tabar wiwi wajen sarrafa magani a Morocco
Wannan dai ya biyo bayan wasu rahotanni da ke yaduwa kan cewa Tinubu ya yi bugun kirji a furucin da ya yi dangane da nasarar da Buharin ya samu a zaben 2015.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce Tinubu ya ce shi ne ya zama ja gaba a yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasara a 2015, “Ba don ni ba da Buharin bai ci zaben ba.”
Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban kasa a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget din APC gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar da za a gudanar a makon gobe.
Wa ya ce na raina Buhari?
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannunsa, Tinubu ya ce ba zai taba yin wani abu da zai lalata alakar siyasarsa da shugaban kasar ba.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce jawabin da ya yi a Abeokuta a lokacin da ya gana da wakilan Jihar Ogun, abokan adawarsa ne suka sauya wa labarin fuska cewa ya raina Shugaba Buhari.
Ya ce furucin da ya yi a Abeokutan tunatarwa ce da kuma fatan hakan zai gamsar da shugaban kasar wajen kawar da duk wata adawa kan muradinsa dangane da zaben fidda gwanin da ke gabatowa na jam’iyyar.
“Bari na kawar da duk wani shakku, akwai girmamawa da mutuntawa da nake yi wa Shugaba Buhari a matsayinsa na Babban Kwamandan wannan kasa kuma a matsayinsa na mutumin da muke da kyakkyawar fahimar juna.
“Ba zan taba wulakanta shi ba kuma tabbas ban yi hakan ba a Abeokuta; Mun kasance abokan siyasa na tsawon lokaci kuma ina fatan hadin kanmu ya ci gaba har nan gaba.
“Ba zan yi wani abu da zan jefa shi cikin hadari ba. Na yi imani jam’iyyarmu [APC] ita ce al’ummar kasar nan ke fatan ganin ta ci gaba da jagorantar kasar nan.
“Na yi imani ina da matsayi mai girma fiye da wanda nake da shi a yanzu; na kuma yi imanin cewa Shugaba Buhari na da muhimmiyar rawar da zai taka ko da wa’adinsa na shugaban kasa ya kare,” inji shi.
Ya kara da cewa ya fito neman takarar shugaban kasa ne da nufin hidimta wa al’ummar Najeriya tare da gamsuwarsa cewa ya dace da zama shugaban kasa, matsayin da ke bukatar sadaukar da kai da kuma samar da jagoranci na gari.
A cewar Tinubu, nufinsa shi ne ya dora a kan kyawawan ayyukan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara.
“Ba na nadamar fitowa neman takarar shugaban kasa, domin kuwa na gamsu cewa ina da muhimmin aikin da zan yi wa ’yan Najeriya, wanda sauran masu neman takara ba su da shi, duk kuwa da cewa ina ganin sauran masu neman kujerar ’yan kasa na gari masu kishi.
‘Ni ba makaho ba ne’
“Duk da cewa ina neman wannan kujerar, amma akwai wasu abubuwa da ba zan yi ba, haka kuma akwai wasu iyakoki da ba zan tsallake ba.
“Ba zan taba wulakanta kaina ba ta hanyar muzanta Ofishin Shugaban Kasa ba; bau yadda za a yi a ce ina neman kujera kuma ina zagin ta,” a cewar Tinubu.
Ya kara da cewa matsayin shugaban kasa ba abu ne da ake bai wa mutumin da bai cancanta ba, haka kuma bai dace mutane su yi kokarin mutumin da ya fi dacewa ya samu matsayin ba.
Zaben gaskiya nake so a yi, inji Tinubu
“Ya kamata mu lura da muhimmacin cewa makomar mutum miliyan 200 ake magana, kuma ni abin da nake bukata shi ne a yi wa kowane dan takara adalci bisa doka da tsari
“Idan har aka yi hakan, kuma ba a zabe ni matsayin dan takarar shugaban kasa ba, ba zan yi korafi ba a kan zaben fidda gwanin, zan karbe shi hannu biyu a matsayina na mai bin dimokuradiyya,” kamar yadda ya bayyana.
Jami’yyar APC dai za ta gudanar da zaben fidda gwani na Shugaban Kasa a tsakanin ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni a Abuja, babban birnin kasar.