✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk wani shirin na durkusar da Gwamnatin Buhari zai gaza — APC

Akwai wadanda ke shige-da-ficen bata wa gwamnatin Buhari suna.

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da cewa duk wasu shirye-shirye da ake gudanarwa da manufar durkusar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba za su kai ga gaci ba.

Sakataren Kwamitin Riko na Jam’iyyar na Kasa, Sanata John James Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai ranar Alhamis a Shelkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

A cewarsa, akwai wasu marasa kishin kasar nan da ke shige-da-ficen bata sunan wannan gwamnati.

Ya ce dukkan wadanda ke kulla tuggun durkusar da wannan gwamnati za su shiga hannu nan ba da jimawa ba kuma za su girbi abin da suka shuka a gaban shari’a.

“Ana iya auna nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta samu a fannin tsaro da sauransu, amma ba zai yiwu a dora ta a kan mizanin mayaudara da masu neman bata wa gwamnatinsa suna ba.

“Wadanda ke biyo wa ta bayan fage da nufin durkusar da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba za su cimma nasara ba.

“Su na duk wani fadi tashi ne don wasu su yi tunanin akwai rashin tsaro a kasar, suna shirye-shiryen durkusar da gwamnatin APC kuma cikin Yardar Allah za su fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata,” a cewarsa.

Ya kara da cewa, Kwamitin Riko na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Bunin a Jihar Yobe, ya kawo zaman lafiya da hadin kai a jam’iyyar kuma kokarin da ake yi yana ci gaba da haifar da kyakkyawan sakamako.