Dan karar shugaban kasa na Jam’iar NNPP, Sana Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce duk wanda ya yake shi a Jihar Kano a zaben 2023, sai ya yaba wa aya zaki.
Kalaman tsohon gwamnan jihar na zuwa ne bayan gwamna mai ci kuma wanda ba sa ga maciji, Abdullahi Ganduje, ya ce wa magoya bayan Jam’iyyar APC, a 2023 Kano za ta maimaita abin da ta yi a zaben shugaban kasa na shekarar 1993.
- An yi garkuwa da DPO a Filato
- Kanawa za su maimata abin da ya faru a Zaben 1993 —Ganduje
- Yadda aka yi wa Sakkwatawa kisan gilla a Anambra
Ana ganin kalaman na Ganduje tamkar gugar zana ce cewa Kananawa ba za su zabi Kwankwaso ba a zaben da ke tafe a ranar 25 ga waan Fabrairu.
Amma a martanin Kwankwaso, ya ce, “Ba na son kula wancan mutumin, ban san ko ya fada ko bai fada ba, amma duk wanda ya yaki NNPP ko Kwankwaso a 2023 sai ya i da-na-sani.”
Ya ci gaba da cewa, “Duk wanda ya san ni, ya san abin da na yi a baya, ya san idan na ci zaben shugabna kasa, Kano za ta fi kowa amfana, Arewa za ta amfana, haka kuma kasa baki daya.”
A cewarsa, “Kwanan nan yi gangamin yakin neman zabe wadanda ke cikin mafiya kayatarwa, ba irin na wasu ’an takara da baki daga wasu jihohi suka shigo ba — Na yi daya a Wudil, Kudancin Kano, daya a Bichi, Arewacin Kano; sannan na bude ofishin yakin neman zabe a Kano ta tsakiya.
“Abin mamaki shi ne wai ni za a ce in kira gangamin yakin neman zabe a Kano; Sau nawa kuma; ko a kwananan daga watan Disamba zuwa Janairun nan na yi; don haka mene ne kaya gabas don ka yi akin neman zabe a Kano?”