✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk tsokar da ta ginu da haram wuta ce makomarta! (2)

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya Fassarar Salihu Makera Daga cikin dukiyar haram akwai cin hanci da rashawa, kuma hakika an la’anci ma’abutanta da masu mu’amala da…

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya

Fassarar Salihu Makera

Daga cikin dukiyar haram akwai cin hanci da rashawa, kuma hakika an la’anci ma’abutanta da masu mu’amala da ita. An karbo daga Abdullahi bin Amru (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya la’anci mai karbar rashawa da mai  bayarwa.” Tirmizi da Abu Dawuda da Ibn Maja suka ruwaito. 

Ma’aikata da yawa a yau ba su jin tsoron Allah, ba su tunanin haduwa da Shi, sai ka ga suna rigegeniya wajen cin hanci da rashawa suna fantamawa a cikin dukiyar rashawa da almundahana.

Hakika magabatan kwarai na wannan al’umma sun san hadarin rashawa da muninta, sun san ita ce sababi na ruguza zaman lafiya da jawo rauni da hallaka da rugujewa ga al’umma da kasa, don haka sai suka bar hanyarta, suka yi nesa da tafarkinta. An karbo daga Sulaiman bin Yassar (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW): Ya kasance yana aika Abdullahi bin Rawaha (RA) zuwa Khaibara, sai ya tsare a tsakaninsa da Yahudawan Khaibara. Ya ce: “Sai suka tara masa wasu kayayyakin kawa na matansu suka ce: “Wannan naka ne, ka yi mana sauki ka kawar da kai wajen rabo.” Sai Abdullahi bin Rawaha (RA) ya ce: “Ya ku taron Yahudawa! Wallahi ku kuna daga cikin mafiya munin halittar Allah a wurina! Me kuke so ku sanya ni a ciki don in saukaka muku? Abin da kuka bijiro min na rashawa lallai ita haram ce. Kuma lallai ba za mu karbe ta ba.” Sai suka ce da (gudun irin) wannan ne sama da kasa suka tsayu.” Malik ya ruwaito.

Ya ku Musulmi! Ku sani daga cikin mafiya muni da hadarin rashawa wadda ta fi cutar da al’umma, ita ce rashawar da aka bayar domin dakile gaskiya ko a tauye hakki, haka rashawar da ake bai wa shugaba ko alkali. An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah ya la’anci mai karbar rashawa da mai bayarwa a cikin hukunci.” Tirmizi ya ruwaito kuma ya ce, Hadisi ne mai kyau ingantacce.

Masruk (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Idan alkali ya ci kyauta (daga masu husuma a gabansa), hakika ya ci haram. Idan kuma ya karbi rashawa sai ta kai shi ga kafirci.” Nisa’i ya ruwaito.

Rashawa tana jawo barna ga zamantakewar jama’a, tana ruguza hakkoki ta jawo hallaka. An karbo daga Amru bin Al-As (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wata al’umma da riba za ta bayyana a cikinta face an rike musu sama-an hada su da fari da rashin ruwa-kuma babu wata al’umma da rashawa za ta bayyana a cikinta face an hada ta da tsawa (bala’o’i).” Ahmad ya ruwaito.

Yau ga shi al’ummarmu tana dandana sakamakon cin dukiyar haram na daga aukuwar yakukuwa (kashe-kashe) da hallaka (kamar girgizar kasa da sauransu) da fari da rashin ruwa. Sama tana rike ruwanta tana hana kasa alheranta, rana tana sako cikakken zafinta, sannan hunturu yana sako tsananin sanyinsa. Don haka ku ji tsoron Allah ku guji abubuwan da suke kawo fushinSa suke jawo ukubarSa. Domin da yawa al’ummar yau tana dandana bala’in yakin da ke cutar da Musulunci da mabiyansa ne saboda cin dukiyar haram.

Kuma daga cikin dukiyar haram akwai roko ko bara, mutum ya roki mutane ba tare da bukata ko lalura ba. Roko sababi ne na janye albarkar dukiya, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku daina yawan roko. Na rantse da Allah babu wani daga cikinku da zai roke ni wani abu, kuma rokonsa ya sa in fitar da wani abu in ba shi ba tare da sona ba, sannan Allah Ya albarkace shi cikin abin da na ba shi.” Buhari ya ruwaito.    

Roko na zubar da kimar Musulunci, yakan rika nuna kamar addini ne na mabarata, hakan kan ba makiya Musulunci dama su rika misali da hakan wajen bata Musulunci. Mabarata suna sauya fasalin masallatai su cika su har su rika zama hadari ga jama’a. Manzon Allah (SAW) ya ce: “dayanku ba zai gushe ba yana rokon mutane har sai ya iske Allah babu tsokar nama a fuskarsa.” Muslim ya ruwaito.

Mutane da yawa a yau suna fama da talauci, yunwa na damunsu amma suna dauriya, su kasance masu kamun kai suna masu kyawawan dabi’u, ba su daga hannuwansu sai ga Allah, ba su mika bukatarsu face ga Allah duk kuwa da tsananin talauci da bukatarsu. Sun kasance kamar yadda Allah Ya siffanta su: “Jahilin halinsu yana zaton su wadatattu ne saboda kamun kai, kana saninsu da alamarsu, ba su rokon mutane da nacewa.” (Bakara:273).

Amma daga cikin mutane akwai wanda yake ta rokon bayin Allah ya bar Wanda taskokin sammai da kasa suke hannunSa, kuma yana rokon ne ba tare da bukata ko rashi ba, a’a sai domin ya yi ta tara dukiya yana taska ce ta, har a wayi gari ya mayar da roko sana’a ko aikinsa na samun dukiya. Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da kun san abin da yake cikin roko (ko bara), da wani bai je ga wani ya roke shi ba.” Nisa’i ya ruwaito.

Kuma (SAW) ya ce: “Mutum ba zai bude kofar roko ga kansa ba, face Allah Ya bude masa kofar talauci. Mutum ya dauki igiya ya tafi saman dutse (daji) ya yi itace ya doro a gadon bayansa (ko ya dauko a ka) ya fiye masa alheri da ya roki mutane, su ba shi ko su hana shi.” Ahmad ya ruwaito.

Sai dai duk da haramcin roko da tsananin ukubarsa a Ranar Lahira, akwai rokon da shari’a ta halatta, kuma ta yi cikakken  bayani a kansa. Wato kamar mutumin da bashi ya hau kansa da mutumin da dukiyarsa ta kare da mutumin da talauci ya yi masa yawa har masu hankalin cikin mutanen da suka san shi suka ce kai wane ya shiga talauci. Wadannan ya halatta su yi bara har sai sun samu natsuwa ko tsayuwa da kafafusu ko sun biya bashi ko bukatunsu. Kamar yadda ya zo a Hadisin kubaisah bin Muharik Al-Hilali da Muslim ya  ruwaito.

Baya ga wadannan duk wani roko haram ne, wanda ya ci abin rokon ya ci haram. 

Wancan Hadisi babban dalili ne na haramta roko ko bara ba tare da bukata ko lalura da ta halatta ba, idan babu lalura roko ko bara haram ne, duk mai cin kayan rokon wuta yake ci a cikinsa. Don haka ku ji tsoron wuta ku bar dukiyar haram. Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai roko ba ya halatta ga mawadaci ko mai karfi mai lafiya, sai dai yana halatta ne ga fakirin da bai da wata hanya ko wanda bashi ya yi wa yawa. Duk wanda ya roki mutane domin dukiyarsa ta karu, zai tashi fuskarsa ba ta da tsoka Ranar kiyama, kuma duwatsu masu kuna zai rika ci daga Jahannama, wanda ya so ya daina, wanda ya so ya ci gaba (da tarawa).” Tirmizi ya ruwaito.

Daga cikin dukiyar haram akwai karbar dukiyar mutane a matsayin rance ko bashi, amma ba da niyyar biya ko mayarwa ba, ko a yi wasa da jan hankali wajen biyan. Wannan zalunci ne da ta’addanci a kan haramce-haramcen Allah. Allah Madaukaki Ya ce: “Kada ku ci dukiyarku a tsakaninku da karya.” (Bakara:188). Kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya karbi dukiyar mutane (bashi) da niyyar zai mayar, Allah Ya ba shi ikon mayarwa. Wanda kuma ya karba da niyyar cinyewa, to Allah Ya tauye shi.” Buhari ya ruwaito. 

Ya ku mutane! Ku sani cin dukiya ta wannan hanya ta haram da muka ambata zalunci ne da ta’addanci, don haka duk wanda ya san akwai dukiyar mutane a hannunsa da suka ba shi cikin kyautatawa, wajibi ne ya mayar ga masu ita. Bai kamata ka saka wa kyautatawa da munanawa ba. Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Allah Yana umartarku da ku mayar da amanoni ga masu su.” (Nisa’i: 58).

Ya ku mutane! Ku sani duk wanda ya ci dukiyar mutane ta hanyar cuta da hila Musuluncinsa da imaninsa ababen tuhuma ne. Abin da ke gaskata haka shi ne fadin Manzon Allah (SAW): “Musulmi shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa, kuma mumini shi ne wanda jini da dukiyar mutane suka aminta daga gare shi.” Muttafakun alaihi.

To ina Musulunci ga wanda mutane ba su kubuta daga hannunsa ba? Ina imani ga wanda bai kiyaye dukiyar mutane? Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku mayar da amanoni ga masu su, ku tuba zuwa ga Allah gabanin ya zamo babu Dinari ko Dirhami, sai dai kyawawan ayyuka ko munana. An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya san ya zalunci wani ya yi kokarin mayar masa kafin a karba masa daga kyawawan ayyukansa, idan kuma ba ya da kyawawan ayyuka sai a kwaso miyagun ayyukan wancan a jibga masa a jefa shi a wuta.” Buhari ya ruwaito.