✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Duk shekara sai na je Umrah:” To sai me?

A wannan karon, hankalina ya dauku ne zuwa ga wasu daga cikin al’ummarmu, musamman masu hannu da kumbar susa, wadanda suka maida zuwa Umra tamkar…

Allazi Wahidun, Allah da girma yake! Irin wadannan yara na neman tallafi, fiye da tafiya Umra!A wannan karon, hankalina ya dauku ne zuwa ga wasu daga cikin al’ummarmu, musamman masu hannu da kumbar susa, wadanda suka maida zuwa Umra tamkar wani abin gasa da kece-raini. Za ka ga suna bayani, suna kara jaddadawa: “Duk shekara sai na je Umra.” Ni kuwa na ce daga nan kuma sai me?
A duk shekara sai ka je Umra, kana barin al’amura masu matukar muhimmanci a kauyenku ko garinku. Domin a lokacin da ka debi makudan kudi ka tafi Umra, a cikin danginka na jini, da ke rayuwa kusa da kai. Wani ma kila kanenka ne uwa daya, uba daya. Wani kuma yayanka ne, amma bai da aikin yi ko sana’ar yi, zaman kashe wando yake yi. Maimakon a ce ka cacike dukiya duk shekara ka tafi Umrah, da kamata ya yi ka tallafa masu da jari, ko dan abin da za su yi wa iyalansa hidima da azumin nan.
“Duk Shekara sai na je Umrah.” Haka ne, kana zuwa Umrah duk shekara, alhali a makwabtanka, akwai mai yin buda-baki da ruwa, shi da iyalinsa ba su da hatsin da za su tanana cikinsu. Da ni ne kai, maimakon in tafi Umra, da sai in taimaka wa makwabcin nan nawa da hatsi da dan abin da zai dadada wa iyalinsa. Babu mamaki ladar da za ka samu, da ta fi ta tafiyarka Umra, tun da Allah na taimakon duk wanda ya taimaki fakiri, balle ma makwabcinka.
“Duk shekara sai na tafi Umrah.” Haka na ji wani na bugun gaba yana fadi a cikin abokansa. Ni kuwa na ce kaico! Ka tafi Umrah duk shekara, amma ga matasa nan a unguwarku suna ta zaman kashe wando, babu aikin yi babu sana’a. Maimakon ka debi makudan kudi ka tafi Umra, da za ka ware Naira dubu dari uku kadai, ka raba wa matasa uku a matsayin jari ko ka koya musu sana’a, lallai da ladar da za ka samu, sai ta fi ta Umra. Dalili kuwa shi ne, idan Allah Ya albarkaci jarin, sai ka ga sun ginu da kafafunsu, sun samu abin rayuwa. Da haka za su yi aure, su kafa zuri’a, sannan kuma su amfanar da al’umma gaba daya. Idan suka yi haka, ka ga ka zama sanadiyyar kafa arziki ga al’umma. Amma sai ba ka yi haka ba, sai ka bige da aikin riya, kana tafiya Umra, kawai domin kece raini da bugun gaba, cewa kai ma wani ne na musamman!
Fadi yake yana kara fadi: “Duk shekara sai na tafi Umrah.” Ni kuwa na ce, me ka amfana daga yin haka, alhali dukiyar al’umma ce kake kwashewa kana bidirin gabanka? A matsayinka na ma’aikacin gwamnati, don ka yi kashe-mu-raba da dan kwangila, ka wawashe dukiyar da za a sama wa al’ummarka ruwan sha ko za a gina musu asibiti, ka handame kai kadai, ka tafi Umrah, me wannan ibadar za ta tsinana maka? Ka tuna, mutum nawa za su fada cikin halin kaka-ni-ka-yi a yankinku a sanadiyyar rashin ruwan sha mai tsafta, tun da ka kwashe kudin da za a samar da ruwan ka tafi Umra? Ko kuwa za ka iya lissafa marasa lafiyar da za su tagayyara, a sanadiyyar kudin maganin da ka kwashe, ka tafi Umra? Ko kuwa za ka iya biyan diyyar rayukan da za su salwanta a sanadiyyar wannan son kai da ka yi, inda ka kwashe kudin al’umma, kawai ka tafi galarin gabanka? Ni kuwa na ce kaico da irin wannan tafiya Umra! Da ka san alhakin da ka dauka, da ba ka yi haka ba. Da ka bar dukiyar mutane, an yi musu aikin da ya dace da ita. Wannan ya fi alheri, da a ce ka kundume ka tafi Umra.
Kuma wani abin takaici ma shi ne, wasu attajiran suna tafiya Umrar ne kawai da nufin guje wa aikin alheri a yankunansu. Da zarar an fara azumi, sai su tarkata iyalinsu, su hau jirgi sai Saudiyya. Za ka samu makwaftansu suna rayuwar talauci, wasu ma da kyar suke samun abin buda-baki. Idan Sallah ta zo ma, haka za su yi bikin ba tare da sabuwar sutura ba.
Da abin samu ne, maimakon tafiya Umrar nan, da kamata ya yi su tsaya gida, su yi amfani da dukiyar nan wajen kyautata wa ’yan uwa da makwabta. Kamata ya yi a ce sun yi amfani da kudin Umrar nan wajen sama wa fakirai abinci mai rai da lafiya, da sun sama masu suturar da za su yi farin ciki da ita a ranar Idi. Babu shakka, irin ladar da za su samu, na tabbatar sai ta fi ta tafiyarsu Umra.
A yau, makarantunmu na boko da na Islamiyya suna cikin matsala. Za ka ga babu kujeru da tebura, wasu ma makarantun rufinsu a kware yake, suna yoyon ruwan damina. Babu isassun littatattafan karatu da sauran kayan aikin koyarwa. Malaman suna cikin takaicin rashi ko karancin albashi. Maimakon a ce attajiran unguwa sun zanzare sun dauki makudan kudi sun tafi Umra, da son samu ne, da sun yi amfani da rabin kudin wajen inganta makarantun nan, musamman wajen tallafar malaman da kuma gyara ko inganta makarantun. Allah kadai Ya san irin gwaggwabar ladar da mutum zai samu wajen bunkasa ilimi. A’a, ba su yi haka ba, sun kwashe sun tafi Umra, kawai don a ce suna zuwa Umra duk shekara. To, an ce kun je Umra, kuma duk shekara sai kun je Umra – to sai kuma me?
Na taba samun labarin wani attajiri, wanda ya ce shi daga yau ya daina zuwa Umra. Wata rana ce ya shirya kudinsa, ya nufi tafiya Umra, sai Allah Ya kaddara ya makara, jirgi ya tashi ba da shi ba, da ya dawo gida, sai Allah Ya sanya masa ilhamar yin sadaka da kudin. A ranar ya sanya aka tara masa fakirai na unguwar, su wajen mutum goma, ya raba musu Naira dubu dari-dari.
A sanadiyyar wannan kyauta daya da ya yi musu, ya ce har shekarar ta dawo ba a daina gaida shi cikin mutunci ba. Ya ce sai ya koma kamar wani waliyyi a unguwar tasu. Kullum suna yi masa addu’a, wasu kuma suka koma kamar surukansa. Haka kuma, cikin fakiran nan, akwai wadanda suka same shi, suka sanar da shi cewa sun mike da sana’i’insu, sun kuma samu alheri mai yawa. Shin da Umurar ya tafi da kudin nan, anya wannan abin alheri da ya samu a yankinsu zai samu? Dalili ke nan duk shekara, maimakon ya tafi Umra da irin wadannan kudade, sai ya ware fakirai yana yi musu hasafi. Wani lokacin kuma sai ya rika gyara makarantun ko ginawa da yashe kwatocin unguwa.
Ni Gizago, ba adawa nake da masu zuwa Umra ba, amma dai a rika sara ana duban bakin gatari. Idan ka je sau daya kuma ka yi aiin Hajji sau daya, to duba dan uwanka, shi ma ka huce masa takaici. Wannan shi ya fi alfanu, fiye da gadarar cewa: “Duk shekara sai na je Umra” alhali al’ummarka da ’yan uwanka suna cikin halin talauci da fatara.
Wannan ra’ayin Gizago ne. Idan ya dace da naka, to mu rankaya rokon Allah Ya kawo mana sauki, Ya sanya mu cikin ’yantattu a cikin wannan muhimmin wata mai albarka na Azumi!
A sha ruwa lafiya!
***
A labarin farin ciki kuwa, Bagizage Bala Abdu Rano 08062415179, ya samu karuwar haihuwar diya mace, an saya mata suna Nana Fatima. (Allah raya ta, Ya dayyaba, amin).
A labarin jajantawa kuwa, PRO na Gizagawan Jihar Neja, Bello Dandin Mahe Suleja 08034275846, yayan matarsa ne Allah Ya yi wa rasuwa. (Allah Ya jikansa da rahama, mu kuma da muka rage, ya kyautata tamu idan lokacinmu ya zo).