Kasar Qatar, wacce za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya a bana ta ce dukkan mata da mazan da suka yi kwanciyar aure a kasar alhalin ba ma’aurata ba ne za su iya fuskantar daurin shekara bakwai.
Kafar yada labaran France 24 ce ta bayyana hakan, in da ta ce Qatar din za ta dauki mataki ga duk wanda ya yi kunnen kashi da wannan doka, yayin zamansa a kasar.
- ‘Yan sanda a Katsina sun ceto budurwa daga hannun ‘yan bindiga
- Miyagu na shirin jefa Najeriya cikin damuwa – Buhari
A cewar Qatar kuma, duk wani nau’i na walimar, ko taro da ya hada da shan giya ko tarayyar wadanda ba ma’aurata ba, shi ma ya haramta a kasar ga kowa da kowa.
“Babu kowanne irin nau’i na sharholiya. Ya kamata kowa ya kiyaye da hakan, sai dai in yana so a sakaya shi a kurkuku,” kamar yadda kafar ta rawaito Rundunar ’Yan sandan na fada a cikin wata sanarwa.
A kasar ta Qatar dai, shan giya a bainar jama’a haramun ne, haka cakudar maza da mata matukar ba ma’aurata ba ne.
Za a fara gasar ce a watan Nuwamba mai zuwa, kuma tuni aka kammala buga wasannin tantance kasashen da suka cancanta su buga gasar.