✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk Kwamishinan da ya ki a rage albashinsa bai son aiki – Ahmed Tijjani

Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Nasarawa, Alhaji Ahmed Tijjani ya ce duk kwamishinan da bai amince a rage masa albashi a jihar ba, ba aiki…

Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Nasarawa, Alhaji Ahmed Tijjani ya ce duk kwamishinan da bai amince a rage masa albashi a jihar ba, ba aiki ya zo yi ba. Kwamishina Ahmed Tijjani ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga ikirarin da wadansu kwamishinonin jihar suka yi cewa idan gwamnatin jihar ta rage musu albashi za su yi murabus daga mukamansu.
Ya ce aikin Kwamishina kamar sauran ayyukan gwamnati sadaukarwa ake yi domin a bauta wa al’umma. Saboda haka a cewarsa abin takaici ne da rashin tunani da son kai a ce masu rike da muhimman mukamai a gwamnati ke yin irin wannan magana. Ya bayyana gwamnatin mai ci a karkashin jagorancin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura a matsayin wadda ta cimma nasarori da dama musamman a bangarorin samar da ababen more rayuwa da suka hada da ruwan sha da makarantu da asibitoci da hanyoyin da sauransu, inda ya kara da cewa a tarihin gwamnatocin jihar da suka shude ba a taba samun wanda ta fi ba da fifiko ga ci gaba da inganta jin dadin ma’aikatanta kamar ta Gwamna Al-Makura ba.
Ya ce “A gaskiya ban yarda cewa wasu kwamishinoni a jihar nan za su iya yin wannan tunani ba, amma idan suna yin wannan shiri, to abin da zan ce shi ne batun shugabanci abu ne da ke son sadaukarwa a koyaushe. Akwai jihohin da kwamishinoninsu ba su ma samun albashi balle a yi maganar rage musu albashin. Amma a nan Jihar Nasarawa gwamnati na iya kokarinta wajen biyan albashi don an dan samu matsalolin tattalin arziki sai su ce za su yi murabus? Haka bai dace ba kuma ba su yi wa Gwamna da al’ummar jihar nan adalci ba.”
Ya shawarci kwamishinonin su sauya tunani, inda ya ce faduwar tattalin arziki da ta shafi kasar nan ta sa gwamnatin jihar ta bi sawun sauran jihohin kasar nan ga daukar wannan mataki ba don ta musguna wa wani ba.
Idan ba a manta ba, a mako jiya ne wadansu kwamishinonin jihar suka yi zaman gaggawa bayan da suka samu labarin gwamnatin jihar na shirin rage musu albashi inda suka ce za su yi murabus daga mukamansu idan gwamnati ta rage musu albashi.