Yayin da hankullan alu’ummar Musulmi a duk fadin duniya ya karkata wajen bukukuwan Karamar Sallah, hasashen masana lissafin taurari na Musulunci na nuna cewa akwai yiwuwar ba za a ga watan ba yau.
Idan hakan ta tabbata, a bana al’ummar Musulmi za su cika azumin watan Ramadan 30 cif-cif.
A wata tattaunawa da ya yi da Aminiya ranar Juma’a, wani masanin taurarin a Kaduna, kuma mamba a Kwamitin Duban Wata na Kasa, Malam Salihu Muhammad Yakub, ya ce bisa la’akari da ka’idar lissafin ganin watan Musulunci, ba zai yiwu ko wacce kasa ta ga watan Sallah ba a wannan rana.
- Yadda Musulmi ke azumin Ramadan da dokar hana fita
- A duba watan Shawwal ranar Juma’a —Sarkin Musulmi
Malam Yakub ya ce, “Ainihi da ma a Musulunci ba wai dole ba ne a ga wata 29 ga wata.
“Dukkan hadisan da suka yi magana a kan ganin wata sun tabbatar da cewa wata kwana 29 ne, kada ku yi azumi sai kun ga wata, kada ku sauke [azumin] sai kun ga wata; amma idan watan ya boyu, to ku cika 30”, inji masanin.
Ka’idar ganin wata
To ko mene ne sharadin ganin jinjirin wata?
“A ka’idar ganin watan Musulunci sai rana ta riga wata faduwa kafin a iya ganinsa.
“Amma a bana wata zai fadi ‘yan mintuna kafin rana ta fadi, wanda hakan na nufin ba zai yiwu a ganshi ba a yau [Juma’a], ko da an yi amfani da na’urar hangen nesa watan wato telescope”, in ji Malamin.
Ya kara da cewa, “Akwai abin da ake cewa ‘Iktiran’ da Larabci, wato haihuwar jinjirin watan.
“Dole sai an haifi jinjirin watan kafin a iya ganinsa. To kuma har ya zuwa yanzu [kusan karfe 12 na ranar Juma’a] ba a ma haife shi din ba ballantana a yi maganar ganinsa.
“Kuma a ka’ida watan sai ya yi akalla sa’a 19 [da haihuwa] kafin a iya ganinsa da ido.
“A yau [Juma’a] a agogon Najeriya sai misalin karfe 6:39 za a haifi watan, ka ga ke nan ba zai yiwu a iya ganinsa a yau ba.”
‘Akwai karancin ilimin taurari’
Da ya juya kan sabanin da ake samu wajen ganin wata, masanin ya nuna damuwa cewa akasarin kasashen duniya ba su cika samun matsala a wajen dauka da kuma sauke azumi kamar yadda Najeriya take samu ba.
Malamin ya alakanta hakan da karancin ilimin lissafin taurari na Musulunci a tsakanin jama’a.
Hakazalika, shi ma da yake nasa fashin bakin, wani masanin ilimin lissafin a Kaduna, Ustaz Isa Aliyu Alfalaki, ya ce Musulmi su shirya yin azumi 30 a bana saboda a ka’idar lissafin Musulunci ba zai yiwu a ga wata ranar Juma’a ba.
Ya kawo hujjoji da hadisai da dama da suka tabbatar da hakan.
Gargadin Sarkin Musulmi
Da ma dai duk da ta bukaci Musulmin Najeriya su fara dubana wata ranar Juma’a, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), a karkashin jagorancin Babban Shugabanta Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ta yi gragdin cewa zai yi wuya a gan shi.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na Majalisar, Farfesa Salisu Shehu, ya fitar ranar Litinin da ta gabata.
A cewarsa, bisa ga shawarar Kwamitin Duban Wata na Kasa, ranar Juma’a 22 ga watan Mayun 2020, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1441, ita ce rana ta farko ta duban watan.
“Sai dai kuma, a wannan yinin, wata zai fadi ‘yan mintuna kadan kafin rana, lamarin da zai sa ganin jinjirin wata ya yi matukar wahala.
“Duk da haka, a bisa koyi da Sunnar Annabi Muhammad, Babban Shugaban na kira ga Al’ummar Musulmin Najeriya da su duba jinjirin wata da zarar rana ta fadi da yammacin Juma’a 22 ga watan Mayun 2020, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1441”, inji Farfesa Shehu.
Shagulgulan Sallah
Musulmai dai a duk fadin duniya su kan yi bukukuwan Karamar Sallah ne bayan kammala azumin watan Ramadan don nuna godiya ga Allah ta hanyar shagulgula, dinka sababbin tufafi da kuma ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki, ko da yake a bana bikin za a yi shi ne ba tare da wadannan shagulgulan ba saboda kalubalen cutar coronavirus.
Ba kasafai dai watan na Ramadan yake cika kwana 30 ba a mafi yawan shekaru, idan kuma wannan hasashen ya tabbata, alu’ummar Musulmin Najeriya ba za su yi Sallah ba ke nan sai ranar Lahadi.