✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk dabarun Buruji ya gaza guje wa mutuwa —Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce mutuwar Sanata Buruji Kashamu izna ce ga kowa domin duk da irin dabarun mamacin ya kasa tsere wa…

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce mutuwar Sanata Buruji Kashamu izna ce ga kowa domin duk da irin dabarun mamacin ya kasa tsere wa mutuwa. 

Obasanjo a sakon ta’aziyyar Buruji ya ce duk da dabarun marigayin na tsere wa shari’ar laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa a ciki da wajen Najeriya, hakan bai sa ya iya tsere wa mutuwa ba.

“Na samu mummunan labari na mutuwar Sanata Esho Junaidu (Buruji Kashamu) wanda mutum ne muhimmi a Jihar Ogun; ina mai mika ta’aziyyata da ta iyalina a kan wannan babban rashi.

“Rayuwa da tarihin marigayin izna ce gare mu baki daya, domin Sanata Esho Jinaidu a lokacin rayuwarsa ya yi ta guje wa fuskantar shari’ar laifukan da ake tuhumarsa da su a ciki da wajen kasar nan.

“Amma da mutuwa ta zo masa babu dabarar likitanci ko ta siyasa ko al’ada da ta hana ta dauke shi a daidai lokacin da Mahaliccinsa Ya yi wa’adinsa ya cika.

“Ina rokon Allah Ya jikan sa, Ya yafe masa, Ya sanya shi a Aljannah, Ya kuma bai wa iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki hakurin jure rashin.