Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) Ayuba Wabba ya fito jagorantar zanga-zangar Kungiyar zuwa Gidan Gwamnatain Jihar Kaduna bayan Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da neman sa ruwa a jallo.
Dubban ’yan kungiyar NLC ne ke biye da Wabba suna tattaki a zanga-zangar lumanar daga Titin Waff a garin Kaduna zuwa Gidan Gwamantin.
- An kama uba yana lalata da ’yar cikinsa
- An kama mata da miji masu safarar jarirai
- El-Rufai na neman Shugaban NLC ruwa a Jallo
- Zan kawo hargisti a zaben 2023 — Igboho
A safiyar Talata El-Rufai ya ayyana shugaban na NLC a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, tare da alkwarin tukwici mai tsoka, bayan NLC ta shiga yajin aiki da zanga-zangar lumana da suka tsayar da harkoki cik a jihar.
El-Rufai wanda ake wa yajin aikin saboda koran dubban ma’aikata, yana zargin Wabba da sauran shugabannin NLC na Kasa da yi wa tattalin arzikin Jihar Kaduna zagon kasa da kuma lalata kayan gwamanti.
Tuni dai kungiyoyoin kwadago daban-daban suka tsunduma yajin aikin da ke kara tasiri a jihar.