’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum tara a Jihar Kaduna, kasa da wata guda bayan gwamanti ta katse layin sadarwa a wasu sassan jihar.
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin, a yammacin ranar Asabar.
- Yadda ’yan IPOB ke tserewa bayan sojoji sun kashe wasu a Anambra
- Bayan kwana 55, Sanata ya kubuta daga hannun ’yan bindiga
“An yi garkuwa da su ne a kusa da Jakaranda kuma masu garkuwa da su na menan Naira miliyan 50; Jiya (Juma’a) aka kira ni daga kauyen, inda ni da shugabanninsu muka gaya musu iya abin da za mu iya a irin wannan yanayi.”
An yi awon gaba da mutanen ne a kauyen Dangilmi da ke kusa da Makarantar Bethel Baptist inda a watan Satumba ’yan bindiga suka sace dalibai 121 a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Rabaran Hayab ya ce, “Dole yau (Asabar) na kira shugabannin makarantar na shaida musu cewa su dakatar da dukkannin abubuwan a makarantar tukuna.”