✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da dokar Buhari ba a dania shigo da shinkafar waje ba —Rahoto

Binciken Aminiya ya gano ’yan kasuwa na ci gaba da hada-hadar shinkafar waje.

Aminiya ta gano cewa duk da dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, har yanzu ana samun ta a kasuwanni fadin Najeriya.

Binciken ya gano sake bude iyakokin Najeriya da aka yi ya taimaka matukar wajen shigo da shinkafar ta barauniyar hanya.

Sai dai wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da ’yan kasuwa sun koka cewa hakan na iya sake mayar kasuwancin shinkafar gidan jiya.

Masu masu sa ido kan harkar kasuwanci kuma na zargin ’yan kasuwa da rashin samar da shinkafa mai nagarta, baya ga tsawwala farashin shinkafa don samun riba mai yawa.

Hakan a cewarsu ka iya maida wa Gwamnatin Tarayya hannun agogo baya na kokarinta na habaka harkar noman shinkafa.

A watan Disamba shugaba Buhari ya ba da umarnin sake bude iyakokin Najeriya, amma wasu ’yan kasuwa sun shaida mana cewa tun kafin bude iyakokin ana samun shinkafar waje a kusan ko’ina.

Yadda lamarin yake a wasu jihoji

Jihar Legas

Rahotanni daga Jihar Legas sun bayyaa cewa ana shigo da shinkafar waje daga kasar Benin, sannan a sake mata buhu tare da sayar da ita zuwa wasu sassan kasar nan.

Yawanci mata ne ke shigo da shinkafar a kananan mazubi sai kuma a sake musu buhu.

Wata mata da wakilinmu ya zanta da ita a Mararrabar Igbolerin, ta shaida ce ana shigo da shinkafar ce ta wata barauniyar hanya da ke kusa da iyakar Seme.

“Ana dakon shinkafar ne daga iyakar Seme Border, inda ake ba masu motar J5 N2,000 a kan kowane buhun shinkafa, su kuma sai kawo su har kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas,”  inji ta.

Wata ’yar kasuwa Khadija Amar, ta ce kasuwancin shinkafa babu riba a cikinsa.

Ta ce, “Shinkafar gida a da muna sayar da ita N20,000 amma yanzu ta dawo N17,500, wasu daga cikinmu suna asarar N3,000 wasu kuma N4,000, shi ya sa muka mai da hankalinmu wajen sayar da ta waje.

“Shinkafar waje tana nan a ko’ina a cikin kasuwa kuma kowa ya sani, an fi sayen ta cikin sauki ba tare da bata wani lokaci ba,” a cewar Amar.

Jihar Ribas

A birnin Fatakwal na Jihar Ribas kuma an jima da ci gaba da kasuwancin shinkafar waje.

Wakilinmu ya gano cewa kusan ko’ina a kasuwannin Jihar mutum zai tarar ana sayar da shinkafar waje.

Wani dan kasuwa da ke kasuwar Mile 1 a Jihar Ribas, ya bayyana cewa ana kawo musu shinkafar waje daga Legas da Kalaba.

Jihar Filato

Wakilinmu a Jihar Filato ya zaga kasuwar Yankwalli inda ya gano ’yan kasuwar na sayar da shinkafar waje a fili ba tare da tsoron ko wani abu zai faru da su ba.

Aminu Mubi, babban dan kasuwa ne kasuwar ta Yankwalli, ya ce tun kafin bude iyakoki, shinkafar waje ta fi ta gida tafiya a wajen masu saya.

“Bayan rufe iyakoki, farashin shinkafa ya kai N27,000 amma yanzu ya sauka zuwa 23,000, kuma muna sa ran zai sake sauka nan gaba kadan,” kamar yadda ya bayyana wa wakilin namu.

Jihar Kano

A wasu manyan shaguna a Kano, ana sayar da shinkafar waje a bainar jama’a ba kamar a watannin baya ba, wanda ake sayar da ita a boye.

A kasuwar Singa da ke Kano, babban buhun shinkafar ana sayar da shi kan farashin N23,500 a maimakon 26,000 da ake sayar da shi a baya.

Sanusi Hassan, dan kasuwa a Singa ya ce “Kasuwancin shinkafar gida yana cikin wani hali, saboda mutane sun fi sayen shinkafar waje.

“Ya kamata gwamnati ta yi wani abu, don hana karyewar kasuwancin shinkafar gida,” inji Hassan.

Abuja

Binciken Aminiya a kasuwannin Abuja ya nuna cewar har yanzu ana sayar da shinkafar waje sosai.

Agatha Ezekie, a Kasuwar Wuse, ta ce yanzu ana sayar da babban buhun shinkafar waje N26,000, shinkafar gida kuma babban buhu kan N19,500.

Jihar Katsina

A jihar Katsina ma abin haka yake, shinkafar waje ce ko’ina a wuraren da wakilinmu ya zaga domin tabbatar da hakan.

Sai dai wasu ’yan kasuwa a jihar sun ce hakan ba shi da alaka da sake bude iyakokin Najeriya da aka yi a watan da ya gabata.

A cewarsu, har yanzu iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar na Jibiya, Kwangwalam da Mai’adua a yanzu a rufe suke.

Wani dan kasuwa, Tasi’u Sani, ya shaida wa Aminiya cewa shinkafar waje da suke sayarwa tsohuwar dauka ce ba ta yanzu ba.

Amma bincikenmu ya gano cewar a kullum ana shigo da shinkfar waje cikin jihar ta Katsina, ta barauniyar hanya da sunan ‘Kayan Hajiya’, wanda ake wuce jami’an tsaro ba tare da an bincika ba.

Manoman shinkafar gida sun koka

Wasu manoma shinkafar gida sun koka kan sake bayyanar shinkafar waje a kasuwannin cikin gida duk da dokar da gwamnati na hana shigo da ita.

Abdullahi Lapai daga Jihar Neja ya ce masu fasakaurin shinkfa na cin karensu ba babba, kuma yanzu abin ya zo musu da sauki tunda an sake bude iyakoki.

Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN), Kabir Ibrahim, ya ce shigo da shinkafar waje na iya mai da Najeriya baya kan kokarin da ta yi.

A cewarsa, safarar shinkafar na faruwa ne da hadin bakin ’yan kasa da kuma jami’an tsaro.

Masu sarrafa shinkafar gida

Wani mai kamfanin casar shinkafar gida, Alhaji Nasiru Yahaya, ya bayyana fargabar da suke cikin game da dawowar shinkafar waje, wanda ya ce ka iya gurgunta kasuwancinsu.

Alhaji Nasiru ya kara da cewa da yawa daga masu sarrafa shinkafa sun ci bashi ne don bunkasa kasuwancin.

“Miliyoyin ayyuka na iya shiga hadari ta dalilin shigowar shinkafar waje, saboda da yawanmu ba shi muka ci muke harkar nan,” inji shi.

Wani dan kasuwa da ke Sabon Wuse kan hanyar shiga Abuja, Nuru Jiya, ya ce shinkafar gida ta bata a kasuwa saboda dawowar shinkafar waje.

Me ya kamata a yi?

Masana da dama a harkar kasuwanci da harkar noma sun tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan matsala.

Mathew Inawole, masani a bangaren Tsimi da Tattalin Arziki, ya ce dole mahukunta su sanya ido kan iyakokin Najeriya, tare da kafa dokar ta-baci kan safarar shinkafar waje.

Mallam Abdullahi Baba, masani a harkar noma, ya ce akwai bukatar gwamnati ta ja hankalin ’yan kasa kan illar cin kayan da aka yi fasakwaurinsu.

Babban Bankin Najeriya (CBN)

Da yake amsa tambayoyin kan cewa ’yan kasuwa ba za su rage farashin kayan masarufi ba sakamakon kudin ruwa da ke cikin bashin da CBN yake ba su, Osita Nwanisobi, ya ce ba a ba wa masu kasuwancin shinkafa bashi karkashin (ABP).

Ya bayyana cewa bashin iya kananan ’yan kasuwa kadai ake ba wa.