Biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na amincewa a sake bude hudu daga cikin iyakokin Najeriya na kan tudu wadanda ke shiyoyin siyasar kasa guda uku ba tare da bata lokaci ba, Aminiya ta gano cewa har yanzu ba komai aka aminec a shigo da shi ba.
Iyakokin da aka sake budewar sun hada da ta Seme a Kudu Maso Yamma, Ilelah da Maigatari a Arewa Maso Yamma da kuma ta Mfun a Kudu maso Kudu.
To sai dai sake bude iyakokin da Gwamnatin Tarayya ta sanar ranar Laraba bai shafi kayayyaki kamar shinkafa, kaji da dai sauran su ba.
Hakan dai na nufin za a ci gaba da shigowa da fitar da kayayyakin bayan shafe watanni iyakokin na rufe, lamarin da ya tsayar da harkokin hada-hadar kasuwanci cik.
Aminiya ta kuma gano cewa labarin sake bude iyakokin ya faranta ran mazauna garuruwan kan iyakokin da dama wadanda ke fatan rayuwa za ta sake komawa kamar yadda take a baya.
Miliyoyin ’yan Najeriya dai sun koka kan yadda rufe kan iyakokin ya jefa su cikin matsanancin talauci, kara ta’azzara tsadar rayuwa da kuma takaita hanyoyin samun kudaden shigar su.
Kazalika, lamarin ya shafi tattalin arzikin makwabtan kasashe kamar Benin, Jamhuriyar Nijar, Chadi, Kamaru Ghana da dai sauransu.
Tun a lokacin dai, gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin taka wa masu shigo da haramtattun kaya da makamai birki da kuma nufin habbaka harkokin noma da tattalin arziki.