✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun ’yan fashi ta cika a Zariya

Dubun wadansu da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suka addabi jama’a a Dumbin Rauga zuwa Gwargwaje a babban titin Kaduna zuwa Zariya…

Dubun wadansu da ake zargin ’yan fashi da makami ne da suka addabi jama’a a Dumbin Rauga zuwa Gwargwaje a babban titin Kaduna zuwa Zariya ta cika inda ’yan sandan da ke sintiri a hanyar suka kama su.

Majiyar Aminiya ta ce wandada ake zargi da fashin da suka shiga hannu su ne Abdulhamid Tanimu da ke zaune a Dumbin Rauga da kuma wani Bafullatani mai suna Muhammad Murtala wanda ya ce shi daga Karu da ke Abuja ya zo don aiwatar da muguwar sana’ar a wannan yankin a bisa gayyatar abokansa.

Majiyar ta ce rana ta baci wa wadanda ake zargin ne da misalin karfe 1: 20 na dare a ranar Talata inda ’yan sanda suka gan su a mota kirar Honda su biyar daya daga cikinsu sanye da kayan sojoji sun saki babbar hanya sun nufi cikin daji. Nan take ’yan sandan suka bi su inda suka tare motar don bincikarsu, amma sai uku daga cikinsu suka ranta a na kare shi kuma Abdulhamid Tanimu ya yi harbi sau biyu amma sai samu kowa ba.

Majiyar ta kara da cewa an samu bindiga kirar AK 47 guda daya da adduna 3 da harsasai da kuma layu da sauransu.

Sun kuma tabbatar da bakinsu cewa su ne suke fitinar wannan yanki da fashi.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya tabbatar wa Aminiya da kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi da fashin tare da bindiga kirar AK 47 da sauran makamai