Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta sanar da cafke mutum 10 da ake zargin da aikata fashi da makami da kuma safarar miyagun kwayoyi.
Ana dai zargin mutanen ne da aikata laifukan a biranen Maiduguri da Jos da Kano da Yola da Abuja da Damaturu da kuma Jalingo.
- Ban ga dalilin barazanar tsagerun Neja Delta ba — Buhari
- Takarar Shugaban Kasa: Fastocin Gwamnan Bauchi sun mamaye Kano
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Bello Makwashi ne ya sanar da hakan ga ’yan jarida ranar Litinin.
A cewarsa, “Ranar 24 ga Afrilun 2021, mun cafke mutum biyu a Kano suna kokarin yi wa mazauna Maiduguri fashi.”
Ya ce sun cafke wadanda ake zargin ne daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 28 ga watan Mayun 2021.
Makwashi, wanda kakakin ’yan sandan Jihar ya wakilta, ya ce rundunar ’yan sandan ta kuma cafke wasu mutum biyar a Maiduguri, Jos, Kano da Jalingo kan satar kudi har Naira miliyan 23.
Ya ce mutum biyun da suka cafke a Kano sun kware ne wajen yi wa mutane fashin kudi.
Ya ce bayan zurfafa bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin satar kudin a wata mota da aka ajiye a kusa da Sakatariyar Musa Usman da ke birnin Maiduguri.
Sannan ya ce, sun amsa yin fashi a Kano, Abuja, Sakkwato, Jos, Damaturu, Zamfara da kuma Jigawa.
An samu adadin kudi har kimanin miliyan 14 daga wanda ake zargin tare da ababen hawa guda biyar da mukullin mota biyar da aka yanka.
“Mun kuma sake cafke mutum biyu da suka kware wajen safarar miyagun kwayoyi a yankin Jajeri da hodar iblis mai nauyin kilo giram 1,005 wacce ta kai darajar kudi miliyan uku da rabi,” inji shi.
Kwamishinan ya ce za a mika wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike a kansu.