Rundunar Jami’an ‘Yan Sanda ta Musamman (SWAT), ta cafke wasu mutum biyu a garin Yenagoa da suka kware wajen kwacen wayar hannu, tare da samun wayoyi 23 a wajensu.
Kakakin ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ne ya shaida wa manema labarai kamun masu laifin a yankin Akenfa yayin da suke kokarin tafiya da wayoyin zuwa jihar Kano domin cin kasuwarsu.
- Gwamnatin Tarayya ta sa ranar bude filin jirgin saman Kano
- An rufe makarantun Birnin Gwari bayan garkuwa da daliban firamare
- Dalilin haramta sinadaran karin dandano a Kano
“An cafke ababen zargin biyu a yayin da suke kokarin tafiya da wayoyin zuwa jihar Kano a wata mota kirar Toyota Hiace.”
“Kwamishinan ‘yan sanda CP Mike Okoli fsi, yana kira ga duk mutanen da aka yi wa kwacen da su je shelkwatar ‘yan sanda don shigar da bayanai da za su taimaka a ci gaba da bincike da bibiyar wayoyinsu.
“A yanzu haka zamu ci gaba da bincike domin gano hakikanin wuraren da suka sato wayoyin kirar Android,” in ji Butswat.
Kazalika, ya ja hankalin jama’a da su guji aikata laifuka, don hukuma ba za ta raga wa duk wanda aka kama da laifi makamancin hakan ba.