✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun wasu barayin da suka addabi mutane ta cika a Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wasu matasa su hudu masu da suka kware wajen shiga gidajen mutane su aikata sata a sassa daban-daban…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wasu matasa su hudu masu da suka kware wajen shiga gidajen mutane su aikata sata a sassa daban-daban na garin Gombe.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ishola Babatunde Babaita, ya ce matasan sun kware matuka wajen shiga gidajen mutane suyi sata da fashi da makami.

Kwamishinan ya ce a ranar shida ga watan Janairun bana ne ’yan sandan shiyyar Tumfure a yankin Karamar Hukumar Akko ta Jihar suka yi nasarar kama matasan.

Wadanda aka kama din sun hada da Isma’il Muhammad mai shekara 21 da ke unguwar Jekadafari da Yusuf Muhammad da ke unguwar Landan Maidorawa mai shekara 21 da Auwal da ake kira da Baban Nana da ba a samu sunan mahaifinsa ba, sai kuma Muhammad mai inkiya da Follo wadanda suka cika wandonsu da iska.

Ya ce ana zarginsu ne da shiga gidajen wasu mazauna unguwar Tumfure, inda suka sace wayar salula kirar Techno Camon 12 da kudin ya yakai N100,000 da kuma agogon hannu.

Kazalika, a wani gidan kuma, ana zarginsu da satar babur kirar Haojue Lucky mai lamba TRN 715 QF da kwamfutoci Laptop guda biyu da kudin su ya haura N600,000 da wayoyin salula guda hudu da kudin su ya kai N72 da sauran kayayyaki.

Babatunde Babaita, ya kuma ce wadanda aka kama din suna da hannu wajen kona gidan wani mutum da ke garin Kwadom a yankin Karamar Hukumar Yamaltu Deba, wanda kimarsa ta kai miliyan 10.

Kwamishinan ya ce rundunar na kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma sannan ya hori al’umma da su dinga kai rahoton duk wasu batagari da basu yarda da take-takensu ba.

Wadanda ake zargin sun amince da laifin su inda ya ce ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala za su tura su kotu.