Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), ta cafke wani da ake zargin dan bindiga ne a Jihar Sakkwato.
Mista Saleh Dada, Kwamandan NSCDC a Jihar ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewar wanda ake zargin mai shekara 40, yana daga cikin wadanda hukumar ke nema ruwa a jallo.
- Lambar NIN: Za a yi wa ’yan Najeriya da ke Amurka rajista
- Shari’ar El-Zakzaky da matsarsa: An tsaurara tsaro a Kaduna
Dada, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata a maboyarsa da ke garin Aliyu Jodi a cikin garin Sakkwato.
Kwamandan ya kara da cewa, an kama shi ne lokacin da ya fito siyan magunguna wadanda galibi na kara karfin maza ne ga mambobin kungiyar tasu.
Kazalika ya bayyana cewa, sun samu nasarar cafke mutumin biyo bayan samun bayanan sirri da jami’an tsaron suka dade suna dana masa tarko.
Kwamandan ya yaba wa al’umma kan yadda suka bayar da bayanan irin kalubalen tsaro a yankunansu tare da ba su tabbacin samun cikakken tsaro.