Rundunar ’Yan Sanda Najeriyya, ta cafke wani mutum yana kokarin satar wata mota mallakin Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa (FRSC) a Abuja.
Kakakin Rundunar na yankin Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya ce jami’an rundunar sun damke mutumin ne bayan wani rahoton gaggawa da suka samu daga dakin tattara bayanai na hedikwatar shiyyar.
- Sojoji sun karkashe mayakan Boko Haram
- Buhari ya gabatar wa ECOWAS rahoton COVID-19
- Sarakunan Arewa na taro kan matsalar tsaro a yankin
Ya ce an sace motar ta hukumar FRSC ce da ke ajiye a ginin tunawa da SKY da ke unguwar Wuse Zone 5 a Abuja, kafin daga bisani jami’an Rundunar na yankin Bwari su cika hannu da mutumin a wani shingen binciken ababen hawa.
“Bayan mun sami kira daga ne dakin tattara bayanai na hadikwatar FRSC sai jami’anmu na yankin Bwari suka samu nasarar cafke wanda ake zargi da sace motar yayin da suke tarewa tare da binciken ababen hawa”, inji Manza.
Ya kuma ce sauran kayayyakin da aka kwace daga hannun wanda ake zargin sun hada da makullin mota guda daya da kuma wata farar mota kirar Hilux Toyota.
Ya ce rundunar na ci gaba da bincike kuma da zarar ta kammala za ta gurfanar da shi a gaban kuliya.