✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun mutumin da yake ƙaryar karɓar Musulunci ta cika a Masallacin Abuja

Mutumin ya saba damfarar jama’a wajen samun taimako da sunan ya karɓi addinin Musulunci.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka fatattaki wani mutumi da ya saba ƙaryar sauya sheƙar addini daga wani masallaci a Abuja.

Wakilin Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya ta takwas, Sanata Shehu Sani ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.

A cewar Sanatan, an kori mutumin daga masallacin ne yayin da asirinsa ya tonu, inda jama’a suka shaida cewa ya saba ziyartar masallatai da majami’ai da sunan karɓar addinin Musulunci ko Kiristanci.

Kazalika, bayanai sun ce mutumin wanda dubunsa ta cika, ya saba damfarar mabiya addinai wajen karɓar gudunmuwar da suke yi masa goma ta arziki a ƙoƙarinsu na ba shi taimako.

“A yau [Juma’a] an fatattaki wani mutumi daga masallaci a nan Abuja bayan jama’a sun shaida cewa ya saba ƙaryar karɓar addinin Musulunci ko Kiristanci a masallatai da majami’ai daban-daban,” a cewar Sanatan.