✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun Mutumin da ya damfari Manoma N2.8m a Jigawa Ta Cika

Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin sa da damfarar manoma N2.8m. Kakakin Hukumar,…

Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin sa da damfarar manoma N2.8m.

Kakakin Hukumar, CSC Adamu Shehu, ne ya tabbatar da hakan a Dutse, babban birnin Jihar, inda ya ce wanda ake zargin mazaunin garin Takai ne da ke karamar Hukumar Jahun.

Ya ce kama mutumin ne ranar 25 ga watan Oktoba, bayan wasu mutane biyu sun shigar da korafi kansa ga Hukumar.

Kakakin ya kuma ce mutumin ya hada kai da wasu mutane biyu, in da yake karbar kudi a hannun manoman da zummar zai kawo musu taki da sauran kayan noma a farashi mai rahusa.

“Daga baya da suka fahimci yaudara ce sai suka yi kokarin ya dawo musu da kudinsu, amma abu ya gagara, shi ne suka kawo kara ofishinmu na Jahun”, in ji Shehu.

Shehu ya ce bayan bincikar sa dai ya amsa laifin, tare da bayyana sunayen wasu mutane hudu da yanzu haka suka ari na kare, kuma da zarar an kammala bincike za a mika su kotu.

Laifin da ake zarginsa da shi dai ya sabwa sashi na 96 da na 320 na kundin Penal Code.