Mutum biyu sun yi kashin kulli 165 na Hodar Iblis din da suka hadidiye bayan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama su a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
- Ni kadai ne zan iya kwato wa PDP mulki daga APC a 2023 – Wike
- Abubuwa 10 da jawabin Buhari ya tabo a Babban Taron APC
Mutanen da aka kama din sun hada da Elvis Uche Iro mai kumanin shekara 53 da kuma Uwaezuoke Ikenna Christian mai shekara 42.
Elvis dai ya yi ikirarin cewa shi mai kawata gidaje ne, amma ya fada safarar miyagun kwayoyi don ya samu jarin fara sana’ar sayar da Coffee.
Ya ce ya yi hakan ne don ya samu ya kula da iyalansa, sannan ya samu kudin makare sabon shagonsa da ke Legas da kaya.
Ya ce ba don kamun da aka yi masa ba, da kimanin Dalar Amurka 1,000 zai samu in ya kai kwayoyin Abuja.
An dai kama shi ne da kulli 65, mai nauyin kilogiram 1.376 na Hodar, bayan saukarsa a filin daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Shi kuwa a nasa bangaren, Uwaezuoke an kama shi ne bayan ya hadiye kulli 100 na Hodar Iblis din, wacce nauyinta ya kai kilogiram 2.243.