✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun mukarraban kasurgumin dan ta’adda ya cika

An rusa gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Kufre Eyo Etim da ake wa lakabi da Romance. Gidan da aka yi lebur…

An rusa gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Kufre Eyo Etim da ake wa lakabi da Romance.

Gidan da aka yi lebur da shi na layin Edim Ita a garin Kalaba, daf da shataletalen tafiya Jami’ar Kimiyya da Fasahar jihar Kuros Riba.

Ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da rikicin kungiyoyin asiri sun addabi jihar musamman ma garin na Kalaba.

Ko a makon da ya gabata ne ‘yan kungiyar asiri suka kashe tsohon shugaban jamiyyar PDP na karamar hukumar Odukpani.

Maharan sun kashe shi ne bayan sun yi masa kwanton bauna a wani wurin da yake shakakatawa a Kalaban.

Da yake yi wa Aminiya jawabi, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Siyasa ga Gwamnan jihar Ani Esin ya ce “Gwamnati ce ta bayar da umarnin rushe gidan.

“Eyo yana cikin jerin mutum 35 da ke hana jihar sakat wadanda jami’an tsaro suke nema ruwa a jallo.

“Mun kama mahaifinsa da wasu mukarrabansa kuma dukkansu suna bayar da da muhimman bayanai,” inji jami’in.