Dubun wasu masu satar mutane ta cika a yayin da suke safarar wani karamin yaro da suka sace suka kuma sanya shi a cikin akwatin gawa.
Sai da masu garkuwar suka yi wa yaron mai shekara 12 sutura da likafani tamkar gawa sannan suka sanya shi a cikin akwatin gawar da suka yi wa huji, inda yaron zai rika shakar numfashi.
- Ya jagoranci kai farmaki kayukan Zamfara saboda kama mahaifinsa
- Abduljabbar zai yi Babbar Sallah a tsare
Yaron, wanda dan asalin kasar Jamhuriyar Benin ne ya shaki iskar ’yanci ne bayan jami’an tsaron Najeriya sun yi arba da motar da aka dauko shi a matsayin gawa a iyakar kasar a Jihar Kwara.
Yaron ba ya cikin hayyacinsa a lokacin da jami’an ’yan sanda da hukumar shige da fice da kwastam da sibil difens suka kama motar gawar karyar ranar Juma’a a Jihar Kwara.
Kakakin hukumar Sibil Difens a Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya ce an kama motar ce a lokacin wani sintiri inda jami’an shiga da fice suka gano direban motar yana neman tserewa.
“Da suka bincika motar sai suka ga akwatin gawa a ciki, ko da suka bude akwatin sai suka ga karamin yaro an lullube shi da likkafani,” inji Babawale.
Ya ce daga nan sai suka sanar da jami’an Sibil Difens da sauran jami’an tsaron da ke sintiri a kan iyakar kasar, kuma ana kokarin ganin an damke mutum biyun da suke tsere daga cikin motar.
“Likitoci sun duba sun kuma tabbatar lafiyar yaron kalau, an kuma gano cewa dan asalin wani kauye ne a Jamhuriyar Benin.
“An damka shi ga jami’an ’yan sanda a kasarsa domin kammala bincike tare da mika shi ga iyayensa”, inji shi.