✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun masu satar mutane don tsafi ta cika a Legas

Da sanyin safiyar Talatar da ta gabata ne dubun wasu mutane da ake zargi da satar mutane da zimmar yin tsafi da sassan jikinsu ta…

Da sanyin safiyar Talatar da ta gabata ne dubun wasu mutane da ake zargi da satar mutane da zimmar yin tsafi da sassan jikinsu ta cika, inda aka gano maɓoyarsu ta ƙarƙashin ƙasa a Legas.

A zantawar da kwamandan rundunan ’yan sanda ta musamman, reshen Jihar Legas, Mista Tunji Diso ya yi da manema labarai, ya shaida cewa jami’an tsaron za su yi amfani da karnuku da ƙwararru don zaƙulo ragowar mutanen da ke cikin ramin. sannan ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali, su ba jami’an tsaro haɗin kai don ganin a cin ma nasara a aikin. Ya ce sun kame mutum uku da ake zargi.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida faruwar lamarin, Malam Nisiru Zurmi ya shaida wa Aminiya cewa da sanyin safiya ne, wata mata daga cikin masu aikin sharar titi tana sharer, da ta zo daidai bakin kwalbatin sai ta jiyo muryar mace da ɗanta daga cikin ramin, tane cewa jama’a su taimake ta, su kawo mata agaji. “Da ta tabbatar da hakan sai ta yi kururuwa, nan take jama’a suka taru a wajan. Nan take ɗaya daga cikinsu ya leko, jama’a suka yi wuf suka kama shi suka cire masa kayan jikinsa suka rufe shi da duka, aka sanya masa taya wutar taƙi ci. Sai wasu suka ɗauko wani ƙaton dutse suka maka masa a kai, nan take ya mutu aka kuma ƙone gawarsa. Daga nan ne jami’an tsaro suka zo aka sake yin nasarar kame wasu mutun biyu daga ramin, ’yan sanda suka tafi da su. Bayan nan wasu ’yan ƙungiyar OPC suka zo wajan suka sanya jan kyalle a hannu suka shiga ramin suka fito da mutum guda suka mika wa ’yan sanda shi. Daga nan wani a cikin dan OPC ya yi yunƙurin shiga ramin sai wani daga cikin ramin ya sare shi a ka, nan ya juyo da baya a guje yana ihu, aka yi asibiti da shi. Daga nan aka sake kama mutum guda a cikin ramin, wanda shi ne ya ba da jawabin cewa sun kai su 24 a ramin kuma sun kwashe sama da shekaru 4 suna aikata ɗanyan aikinsu a wajan,” inji shi.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, jami’an tsaro da jama’ar gari ne suka yi wa ramin ƙofar rago tun daga safiyar Talata har zuwa ranar Laraba.