Rundunar ’Yan Sanda ta Kano ta sanar da kame wasu matasa biyu a filin Sukuwa da ke Kano da take zargi da kwacen wayoyin mutane.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kamen matasan a ranar Laraba.
- Rarara: Ina wakar Buhari da ’yan Najeriya suka biya kudade?
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
- Yadda masu kwacen waya ke cin karensu ba babbaka a Kano
- Yadda Kwamandojin ’yan bindiga suka tuba a hannun Dokta Gumi
“Mun yi nasarar kama wadannan matasa su biyu a filin Sukuwa da ke nan Kano, sun kwaci wayoyin mutane ta hanyar yi musu barazana da wuka.
“Yayin da suke tsaka da kwacen wayoyin muka samu labarin, nan take Kwamishinan ’Yan Sanda Habu A. Sani ya ba da umarnin kamo matasan.
“Ba bata lokaci tawagar ’yan sandan ‘Kan kace Kwabo’, karkashin jagorancin Bashir Musa Gwadabe, suka yi nasarar kamo su.”
Ya ce daya daga cikin matasan mai shekara 29 mazaunanin unguwar Danladi Nasidi ne, sai kuma wani mazaunin Yakasai mai shekara 18.
Yayin kwatar wayar, matasn sun yi wa wani mutum rauni tare da awon gaba da jakar matarsa.
Da yake tattaunawa da wakilinmu, Abdullahi Kabiru ya bayyana yadda matasan suka yi masa rauni da wuka a hannu lokacin da suka kwace masa waya.
“Muna kan hanyarmu ta dawowa daga unguwar Brigade, mun iso daidai Filin Sukuwa sai muka hangi matasa da yawa kamar za su tsallaka titi.
“Ba mu ankara ba sai muka ga sun far mana, sun zare wukake nan da nan suka shiga kwace wa mutane wayoyi.
“Ina kan babur na goyo matata sai suka kwace mata jaka, ina kokarin ba su wayata ne sai daya daga cikinsu ya kawo min sara da wuka, garin kaucewa ya yanke ni a hannu,” cewar Kabiru.
Ya kara da cewa adadin matasan da ya kai 30, sun tare mutane da dama sannan suka kwace musu wayoyi da jakunkuna.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba da umarnin mayar da matasan Sashen Binciken Manyan Laifuka da ke hedikwatar ’yan sandan Jihar da ke Bompai.
Kwacen waya abu ne da ya zama ruwa dare a Kano, wanda a dalilin haka mutane da dama sun rasa wayoyinsu, wasu an musu rauni, wasu kuma sun rasa rayukansu a dalilin hakan.