✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun manomin da ya zuba guba a rijiyoyi 9 ta cika

Manomin dai ya ce ya aikata hakan ne da zimmar hana makiyaya shiga gonarsa.

’Yan sanda a Jihar Yobe sun tabbatar da kame wani manomi dan shekara 25 bisa zarginsa da zuba guba cikin rijiyoyi tara a wani kauye mai suna Kasesa kusa da Damaturu, Babban Birnin Jihar

Kakakin rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, shi ya bayyana hakan  ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a Damaturu  ranar Alhamis.

Ya ce, “Ranar 25 ga watan Mayu, mutumin ya zuba maganin kwari a cikin rijiyoyi tara wanda suka kasance hanyoyin samun ruwa ga mazauna kauyen da dabbobinsu.

“Da muka dauki ruwan rijiyoyin muka kai dakin gwaje-gwaje, mun gano cewa ruwan ya gurbata da sinadarin Fecal Coliforms, wanda yake haddasa amai da gudawa da zazzabin taifod da ma wasu cututtukan da ke da jibi da ruwa.

“A lokacin ne muka nemo wanda ake zargin sannan muka kama shi a yau [Alhamis]. 

“Za mu gurfanar da shi gaban kuliya nan ba da jimawa ba,” inji kakakin.

Jami’in dan sandan ya ce tuni wanda ake zargin ya amince da aikata laifin, amma ya ce ya aikata hakan ne da zimmar hana makiyaya shiga cikin gonarsa.

Kakakin ya ce rundunar tana kokarin kamo makiyayan domin tuhumar su da ketare iyaka.

Sannan ya shawarci manoma da makiyayan da su guje wa ayyukan tada zaune tsaye.