✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun mai yi wa kananan yara fyade a Filato ta cika

An cafke mutumin da ya yi wa kananan yara fyade a Filato

Mazauna garin Bukuru a Jihar Filato sun cafke wani mutum da bisa zargin ya yi wa kananan yara bakwai fyade.

Shugaban matasan garin Bukuru da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, Aliyu Hassan El-Yakub, ya tabbatar wa Aminiya cewa mutumin da dubun tasa ta cika yana tsare.

“Bayan gudanar da binciken a kan wata waya da ya ba wa wata karamar yarinya, sai muka gano cewar ya yi lalata da kananan yara, yawancinsu masu shekara 13 kuma sun tabbatar cewa ya yi musu fyade.

“Bayan kama shi sai muka mika shi ga ofishin ’yan sanda na Bukuru, daga baya kuma aka mayar da shi hedkwatar ’yan sanda da ke Jos,” cewar El-Yakub.

Ya ce mahaifiyar daya daga cikin yaran da aka lalata ta ce, bayan ta ga ’yarta da waya, sai ta sanar da ’yan banga su yi bincike a kan lamarin.

Bayan an gudanar da bincike ne aka gano hakikanin abin da ke faruwa.

Shugaban matasan, ya ja hankalin iyaye da su rika lura sosai da ’ya’yansu, saboda kar su fada a hannun bata-gari da ke yi wa yara fyade.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel, amma ya ce zai bincika ya yi wa wakilinmu bayani.

Sai dai ya zuwa lokaci da muka kammala wannan rahoto, bai waiwaye mu ba.